Bmeri Aboki Ya Samu Lambar Yabo A Jami’ar Bayero

Jamiyar Bayaro ta karrama mawaki Bmeri Aboki, Anyi bikin karramawa mawakin wanda mazaunin Lagos ne a cikin sabuwar jamiyar B.U.K dake jahar Kano, inda bayan gudanar da wasa a gaban masoya da dalibai da dama ne aka mika masa karramawar.

Mawakin wanda raban shi da jahar kano tun a watar faburaru na wannan shekarar yayi godiya ga Allah da samun wannan girmamawa, sannan ya godewa masoyan sa da ma duk wani mai taimaka masa ta kowace hanya.

Mawakin yayi wadan su wasannin a Kano sannan yayi hira da gidajan talabijan da radiyo daban daban.

Mawakin wanda wakar sa ta Mele take a lanba ta daya a cikin shirin zafafa ta gidan tashar talabijan ta Arewa 24 wanda a lokacin daya shigo Kano ya sadaukar da karramawar ga iyayan sa dasu ka rasu, sai iyalan sa, abokanen sa, yan uwansa dakuma masoyan sa.

 

Exit mobile version