Daga Muhammad Maitela,
Biyo bayan farmakin da mayakan Boko Haram suka kai a garin Gaidam ranar Laraba, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya umurci hukumar SEMA ta kai wa jama’ar da farmakin ya shafa tare da kokarin gano kimar asarar da harin ya haifar.
Ranar Laraba mayakan sun farmaki garin Gaidam ranar dauke da makamai masu sarrafa kansu, wanda ya jawo asarar dimbin dukiyar jama’a.
Gwamna Buni ya sanar da hakan ta hanyar ofishin Daraktansa na yada labarai, Mamman Mohammed, Buni ya fara da bayyana alhininsa ga jama’ar Gaidam dangane da harin wanda ya bayyana a matsayin wanda ya mayar da hannun agogo baya a ci gaban da ake samu na maysalar tsaro da kokarin jihar wajen sake farfado da yankunan da abin ya shafa a baya.
Bugu da kari, ya umurci jami’an SEMA su garzaya zuwa garin domin bayar bai wa jama’ar Gaidam agajin gaggawa tare da kiyasta asarar da farmakin ya jawo.
A nashi bangaren, shugaban SEMA, Dr Mohammed Goje, ya shaidar da cewa tuni sun fara aiwatar da umurnin Gwamnan tare da bayar da tabbacin fara aikin tattara bayanai dangane da farmakin da ayyukan jinkan jama’a.
A nashi bangaren kuma, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan-sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa manema labarai a jihar tabbacin kai harin tare da dawo da doka da oda a garin.
Ya ce an kona motoci guda biyu wadanda suke kyautata zaton na mayakan Boko Haram ne a lokacin artabun.
“Haka kuma, yan ta’addan sun kona gida tare da shaguna guda uku, tare da sace magunguna daga babbar asibitin garin da mota kirar Hilux daya mallakar jami’an tsaron jar-kwala.”