Lawal Umar Tilde" />

Boko Haram: Gwamna Lalong Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Ma’aikatan Jinkai 

Gov. Simon Lalong

Shugaban gwamnonin jihohin Arewa 19 kuma Gwamnan jihar Filato Rt.Honarabul Simon Bako Lalong, ya yaba da namijin kokari da jami’an tsaro ke yi a yakin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a jihohin Arewa maso Gabas.
Gwamna Lalong, ya yi wannan yabo ne a cikin takardar da babban jami’in hulda da jama’a na gidan gwamnatin jihar Dakta Makut Simon Macham, ya rabawa ‘yan jarida a Jos a karshen makon da ya gabata, ya ce ya yi matukar farin ciki da jin labarin jami’an cewa tsaro sun yi nasarar kubutar da ma’aikatan sa kai guda biyar dake aiki a sashin jihohin Arewa maso Gabas, tare da ma’aikaciyar kiwon lafiya ta jihar, Jenifer Ukambomg da ‘yan kungiyar ‘yan Boko-Haram, suka sace a watannin da suka gabata.
Gwamna Lalong, wanda tun da fari ya tabbatarwa ‘yan uwan Jenifer, cewa zai yi duk abin da zai iya don ya ga an kubutar da ma’aikaciyar kiwon lafiya din, ya kuma nuna farin cikinsa bisa nasarar da jami’an tsaron ke samu a yakin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta adda a kasar, ya roki al’ummar kasar da su kara bai wa jami’an tsaro hadin kai don su kara samun nasara bisa yakin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a fadin tarayyar kasar nan.  Lawal Umar Tilde

Exit mobile version