A ci gaba da samun kai sabbin hare-haren mayakan Boko Haram a jihar Borno, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umurci shugabanin kananan hukumomin jihar da cewa su hada hannu wuri guda tare da jami’an tsaro wajen aikin tunkarar kalubalen sabbin hare-haren da mayakan Boko Haram ke yi a yan kwanakin nan.
Bugu da kari kuma, Gwamnan ya bayyana matukar damuwar sa dangane da koma bayan lamarin tsaro da ake samu a jihar a yan kwanakin nan, musamman a wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Askira-Uba a jihar.
A cikin makon nan ne dai mayakan na Boko Haram suka kai sabon farmaki a garin Chul, da mabambantan hare-hare a wasu garuruwa irin su Rumirgo, Lassa, Mussa, Kufa tare da Gwandam, duk a cikin karamar hukumar Askira-Uba.
Gwamnan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar bayanin manema labarai, mai dauke da sa hannun mai taimaka masa ta sha’anin sadarwa da yada labarai-Malam Isa Gusau, inda ya ce, Gwamna Zulum ya bayyana hakan dangane da yanda maharan ke takure a yankin arewacin jihar Borno, amma kuma za su iya ratsa kowane bangaren jihar.
Mista Gusau ya ce, “Gwamna Zulum ya damu matuka dangane da ci gaba da kai hare-haren Boko Haram suka aiwatar a garuruwan Chul, Rumirgo, Lassa, Mussa, Kufa da Gwandam, duka a cikin karamar hukumar Askira-Uba da ke jihar Borno”.
“Kuma gwamnan ya bayyana tabbacin goyon bayan gwamnatinsa ga jama’ar da wannan lamarin ya shafa, musamman ta fuskar baiwa sojoji kwarin gwiwa hadi da sauran jami’an tsaro, don ci gaba da kasancewa a yankunan don aikin samar da tsaro tare da samun taimakon yan banga da mafarauta da cibilian JTF a dukan wadannan yankuna”.
“A hannu guda kuma, Gwamna Zulum ya umurci daukwacin shugabanin kananan hukumomin jihar a koda yaushe su ci gaba da aiki kafada da kafada tare da jami’an tsaro a yankin su, domin samun nasarar dakile kalubalen tsaron da ya ki ci ya ki cinyewa kana da daukar ingantattun matakan kare rayuwar jama’a da dukiyoyin su, aiki mafi muhimmanci wanda ya rataya a wuya gwamnati”. In ji shi.