Bello Hamza" />

BOKO HARAM: Kamaru Za Ta Girke Dakaru Kan Iyakar Kasar Da Nijeriya

Kasar Kamaru ta ce za ta girke sojojinta a kan iyakar arewacin kasar da Nijeriya da kuma iyakar yammacin kasar dake yankin masu amfani da harshen Ingilishi, biyo bayan wasu sababbin hare hare da Boko Haram suka kai a arewa da kuma yankin na ‘yan awaren kasar.
Ma’aikatar sojin Kamaru ta kira sojoji su taru a hedkwata a babban birnin kasar Yaoundé kafin babban aikin da za su yi.
Babban hafsan ma’aikatar tsaro Lt. Gen. Rene Claud Meka ya ce, a wannan shekarar ta 2019 Kamaru za ta yi yaki domin hadin kan kasar da kuma tsare mutuncin iyakarta.
Ya ce, sun sake girke dakarunsu a duk wuraren da ake samun tarzoma. Ya ce, ‘yan ta’addan Boko Haram dake Nijeriya suna kuma sake daukar mayaka daga Kamaru suna kuma kai hari a iyakar arewacin kasar. Ya ce, a hali da ake ciki kuma ‘yan aware masu fafutukar ballewa daga yankin masu amfani da harshen Ingilishi su kuma suna daukar mayaka domin tada hargitsi a Kamaru.
Ma’aikatar sojin Kamaru tace Boko Haram tana sake gudanar da ayyukanta a kan iyakarta da Nijeriya a arewacin kasar. Ta kuma bayyana cewa an kai hare hare sau biyar a kan iyakar da kuma tafkin Chadi a cikin wannan wata.
Mayakan ‘yan awaren kuma sun kara kaimi a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi da suka hada da arewa maso yamma da arewa maso gabashin kasar. Sojan kasar ta ce an kashe ‘yan tawayen 45 a makwannin ukun farkon wannan shekara. Su kuma ‘yan awaren sun ce sun sake kashe sojojin.
Koda yake ba a iya bada takamammen adadi ba, amma mazauna kauyukan sun tabbatar da fadan ya kara ta’azzara a cikin wannan lokaci.
Wata ‘yar shekaru 27 da haifuwa tace an kashe ‘ya’yanta guda uku a cikin wani gagarumin fada a garin Buea dake kudu maso yammacin kasar kana bata san inda mijinta yake ba.
Tace wata motar daukar marasa lafiya ta ambulan mallakar wani asibitin cocin Katolika ce ta taimaka mata da wasu mata hudu ta arce da su daga inda sojojin Kamaru da mayakan ‘yan awaren suka yi bata kashi.
Ana zargin ‘yan awaren da suke fafutukar ballewa a yankin masu amfani da harshen Ingilishi ne ta zama kasa mai cin gashin kanta da satar mutane da kashe abokan gaba da kuma kokarin hana gwamnati gudanar da ayyuka a yankunan.
Ministan tsaro Joseph Beti Assompo yace shugaba Paul Biya shi kuma ya bada umarni a jibge runduna a iyakar gabashin Kamaru. Ya ce, fadan da ake gwabzawa a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika yasa an samu karin miyagun ayyukan a wurin.
Ya ce, wannan shekarar 2019 ba za su yi bacci ba. Ya ce, za su ci gaba da ayyuka a arewa mai nisa da yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da kuma sabonta ayyuka na musamma a yankin Adamawa, inda kungiyoyin miyagu na wurin suka kware wurin garkuwa da mutane da kuma neman kudin fansa.
Kasar Kamaru ta ce, sama da mutane dubu daya da dari biyu aka kashe tun lokacin da rikicin ‘yan aware ya barke a shekarar 2016 kana wasu dubu dari biyu da hamsin suka rasa muhallansu.

Exit mobile version