A kokarinta na sake bullo wa lamarin yaki da boko haram ta bayan gida domin samun nasara, Rundunar Sojin Nijeriya ta kaddamar da wata sabuwar dabarar yaki mai suna “Operation TURA TA KAI BANGO”.
Kamar yadda Babban Hafsan Horaswa a rundunar, Manjo Janar NE Angbazo ya bayyana, sabuwar dabarar za ta taimaka wajen kawar da barazanar da sababbin hare-haren boko haram da ISWAP ke yi a yankin arewa maso gabas.
Babban Hafsan Horaswar wanda ya wakilici Shugaban Rundunar Sojin, Laftnar Janar Tukur Yusuf Buratai a wajen kaddamar da sabuwar dabarar a shalkwatar birged da ke Buni Gari a Jihar Yobe, ya ce dabarar za ta zama hayaki fid da na kogo ga ‘yan boko haram da takwarorinsu daga mabuyarsu tare da cafke su ko gamawa da su domin ‘yan kasa su samu sukunin kai komo.
“Operation TURA TA KAI BANGO tana da sabon tsaro na tsaro ta yadda za ta kara wa jarumai kaimi a karkashin dabarar yaki ta operation Lafiya Dole domin dakarun sojin Nijeriyar su ji dadin fatattakar sabbin barazanar da boko haram da ISWAP ke yi a yankin arewa maso gabas na kasar nan. A karkashin sabuwar dabarar, za a mayar da hankali ne kacokam a kan mabuyar tsageran… a karshen lokacin da aka diba na amfani da dabarar, ana sa ran ‘yan kasa za su samu walwala ta kai komo tare da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar noma da kasuwanci cikin kwanciyar hankali,” in ji Manjo Janar Angbazo.
Rundunar dai ta ce tuni aka fara aiki da sabuwar dabarar a ranar 3 ga watan Janairun 2021 kuma har abin ya fara haifar da da mai ido.