Muhammad Maitela" />

Boko Haram: Sabbin Shugabannin Tsaro Sun Yi Wa Maiduguri Tsinke

A karon farko bayan da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya, sun kai ziyarar aiki a cibiyar yaki da Boko Haram ta Lafiya Dole (Theatre Command) da ke birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a ranar Lahadi.

Sabbin manyan hafsoshin sojojin, wadanda su ka kunshi Babban Hafsan Tsaron kasa, Manjo Janar Lucky Iraboh; Babban Hafsan Dakarun kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Babban Hafsan Dakarun Sama, Air bice Marshal Isiaka Amao, hadi da Babban Hafsan Dakarun Ruwa, Rear Admiral Auwal Gambo, tare da sauran manyan kusoshin shalkwatar tsaron kasar.
Bugu da kari, ana sa ran za su gudanar da muhimman tarukan keke-da-keke tare da duk wani mai ruwa da tsaki wajen samun madafa da kara wa juna sani dangane da matakan da suka dace a dauka kan yakin da ake yi da matsalar tsaron.
Har wala yau, wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, ana kyautata zaton za su yi amfani da wannan ziyarar ne wajen tattauna kwararan batutuwa tare da fitar da sabbin matakan da za a fuskanci yaki da matsalar tsaron tare da kai wa ga samun cikakken zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas bakidaya.
A hannu guda kuma, bayan kammala kai ziyarorin da sabbin shugabannin sojojin suke gudanarwa, wanda ya hada da sharkwatar bayar da umarni a aikin sojoji tare da sansanin sojoji na din-din-din a barikin Maimalari dake birnin Maiduguri, kana kuma sun ziyarci Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, hadi da fadar Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi, a duka a lokacin ziyarar tasu.

Exit mobile version