Muhammad Maitela" />

Boko Haram: Sojoji Sun Shawarci Maziyarta Yankin Arewa Maso Gabas

Mazauna Kauye

Rundunar sojojin Nijeriya ta shawarci jama’ar da ke tafiyetafiye da kai ziyara a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, da su rinka tafiya da shaidun da zasu fayyace bayanan su.
Rundunar sojojin ta bayyana daukar wannan matakin a wata takardar sanarwar manema labarai, ranar Asabar; a wani sabon matakin da rundunar sojojin Lafiya Dole ta bullo dashi mai taken “Operation Positibe Identification” a kokarin datse tudadar da mayakan Boko Haram/ISWAP wadanda ke gujewa samamen da sojojin ke yi zuwa wasu garuruwa.
Furucin kanda ya fito daga ofiahin mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin, Ado Isa, inda ya yi wa jama’a kaahedin cewa su rinka yawo da wasu alamu da ke dauke da cikakken bayanan su, a cikin wadannan jihohin.
Isa ya kara da cewa rundunar sojojin ta tsara aiwatar da wannan samamen domin gudanar da binciken kwakwaf tare da cabke yan Boko Haram din da take zargin, wadanda ke arcewa daga yankin arewa maso gabas, bayan tarwatsa maboyar da ta yi.
“Har wala yau kuma, rundunar sojojin Nijeriya tare da bangarorin jami’an tsaro suna farin-cikin samun cikakken goyon bayan yan kasa kan wannan samamen”

Exit mobile version