Muhammad Maitela" />

Boko Haram Sun Halaka Masu Sana’ar Gawayi 18 A Borno

Tafkin Chadi

Majiyar jami’an tsaro a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar masu sana’ar gawayi da itace 18, a wani harin da mayakan Boko Haram suka kai ranar litinin a karamar hukumar Jere dake jihar Borno.
Majiyar wadda ta fito daga wani jami’in ‘yan sanda, ta shaidar da cewa, mayakan sun kashe wasu daga cikin wadannan mutanen ne ta hanyar fille musu kai, yagin da wasu aka kona su har lahira.
Bugu da kari kuma, wasu ganau sun bayyana cewa maharan sun yiwa masu zuwa saran iatacen tare da gawayin kwanton bauna a dajin kauyen Koshebe dake karamar hukumar, mai yar tazara a wajen babban birnin jihar, Maiduguri.
Jami’in ya ce, “maharan wadanda ake kyautata zaton Boko Haram ne sun yiwa masu zuwa saran itacen tare da gawayin kwanton bauna a yankin Koshebe, wanda yake a cikin karamar hukumar Jere ta jihar Borno”.
“Kuma wannan harin ya ci rayukan mutum 18 ne, amma kuma gawawakin mutane 10 ne kawai jami’an tsaron mu tare da hadin gwiwar ‘yan-sintiri (Cibilian JTF) aka gano”.
“Yayin da kuma ba a gano sauran gawawakin mutum takwas ba, lamarin da ke da nasaba da rashin kyaun yanayin yankin da harin ya afku”. Ta bakin majiyar.

Exit mobile version