Boko Haram sun sace ma’aikacin hukumar ayyukan jikai ta majalisar dinkin duniya (UNHCR) tare da sakataren kungiyar dalibai ta kasa reshen jihar Yobe a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno.
Matasan guda biyu da aka yi garkuwa dasu su ne Abubakar Idris da Mua’zu Bawa, wadanda su ke kan hanyar su daga Damaturu zuwa Maiduguri, a sa’ilin da su ka yi kicibis da yan ta’addan sun giciye kan hanyar.
Majiyar jami’an tsaron sa-kai na Cibilian JTF a birnin Maiduguri ta bayyana cewa, an yi garkuwa da matasan ne da misalin 8:30 da safiyar ranar Asabar, tsakanin kauyen Matari wanda yake tsakanun garuruwan Jakana da Auno- a kan babbar hanyar.
“Maharan sun farmaki matafiyan sanye da kakin irin na sojojin Nijeriya, kuma kafin hakan sai da suka datse hanyar da motoci uku kirar Hilud da mashinan hawa.” Ta bakin Cibilian JTF.
Bugu da kari, Hamidu Isa, daya daga cikin yan sintirin da ke aikin tsaro yankin Jakana da Mainok, ya ce, “Bayan da su ka tare motocin, sun rinka binciken fasinjojin wanda bisa ga hakan ne shi Idris ya yi kokarin jefar da ‘ID card’ dinshu, wanda a wannan yanayin ne dayan maharan ya nuna shi.
“Hakan ke da wuya sai su ka bukaci ya fito tare da fasinjoji biyu, kana daga bisani su ka umurci sauran matafiyan su ci gaba da tafiyarsu.”
“Sai dai daga baya maharan sun sako fasinjoji biyun wanda ana sa ran sun sako su ne saboda kila maras abin hannu ne kula kila babu wani aikin da za su yi dasu a dajin Sambisa.”
Malam Isa ya kara da cewa, mafi yawan farmaki da garkuwa da jama’a da ya faru a shekarar da ta gabata, ya na faruwa ne a kan hanyar wanda tazarar bai wuce kilomita 40 ba; daga Maiduguri zuwa Jakana.
Ya ce, hakan ya na faruwa ne a lokacin da su ka faki idon sojoji tare da datse hanyoyin kamar shingen binciken ababen hawa a wuraren da ba kasafai ake yin su ba a Mainok; maimakon Garin Kuturu wanda daga nan hanya ce wadda ta mike zuwa Tabkin Chadi da dajin Sambisa.
Haka zalika kuma, wannan hanya ce wadda mayakan Boko Haram su ka sha kai munanan hare-hare tare da awon gaba da matafiya. Ko a mako biyu da su ka gabata an yi garkuwa da mutum 35 a kan hanyar.