Muhammad Maitela">

Boko Haram Sun Yi Garkuwa Da Matafiya 35 A Kan Hanyar Damaturu-Maiduguri

Majiyoyin da wakilinmu ya tattara sun bayyana yadda wasu mayakan da ake kyautata Boko Haram ne sun yi awon gaba da akalla matafiya 35 a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Bugu da kari, bayanan sun kara da cewa, maharan sun farmaki kwambar motocin matafiyan kusa da Garin- Kuturu wanda yake dab da garin Jakana, a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da misalin 5:00 na yammacin ranar Jummu’a.

A hannu guda kuma, maharan sun harbe wata mata har lahira; a cikin motar safa-safa ta ‘Borno Edpress’ tare da cinna wa motoci bakwai wuta a lokacin da su ka kai wannan harin.

Ganau a farmakin ya bayyana cewa yan ta’addan sanye da kakin sojoji, sun datse babbar hanyar wadanda suka zo da motoci kirar Hilud biyar, wanda daga nisani su ka yi awon gaba da matafiyan.

Majiyar ta kara da cewa, “Da farko matafiyan sun hango hayaki, wanda a zatonsu wutar daji ce, ashe yan ta’adda ne suka yi wa direban motar dakon kaya ta kamfanin Dangote kwanton-bauna inda kuma suka cinna mata wuta.”

“Wanda karasuwar su kusa da inda motar ke da wuya, kan ka ce me sun fada tsakiyar maharan dauke da muggan makamai, sannan kuma da suka ga hakan sun yi kokarin ja-da-baya, amma ina, saboda a daidai wannan lokacin maharan sun riga sun yi musu kofar rago.”

“Sannan a hakan wasu fasinjojin su ka tsallake rijiya da baya; su ka gudu cikin daji, amma sun yi awon gaba da 35, sun kona motocin da ba na haya ba biyu tare da babbar mota daya. Haka kuma an bar motoci tara na mutanen da aka yi garkuwan da su a wajen, kana daga bisani kuma an wawushe kayayyakin su.” In ji majiyar wanda bai yarda a bayyana sunan shi ba.

Exit mobile version