Connect with us

LABARAI

Boko Haram Sun Yi Wa Modu Sheriff Kwambar Kwanton-bauna

Published

on

Maharan Boko Haram sun halaka mutum biyar kisan gilla a wani harin kwanton- bauna da su ka yi wa kwambar motocin tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, inda su ka kashe mutum biyar, a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

A wata majiyar tsaro ta bayyana yadda maharan su ka kai wa motocin Sheriff farmakin, kusa da garin Auno, yan kilo mitoci daga Maiduguri.
Har ila yau kuma, wata majiya ta kut da kut da Ali Sheriff ta nuna cewa lamarin ya faru ne a kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri daga Abuja da yammacin ranar Alhamis, ranar uku bayan rasuwar mahaifinsa, Galadima Sheriff, wanda Allah ya yi wa rasuwa makon da ya gabata.
Ya kara da cewa, Sanata Sheriff wanda ya ke kan tafiyar tasa tare da motocin alfarma guda tara.
Har ila yau kuma, majiyar ta kara da shaidar da cewa, tawagar tsohon Gwamnan, ta yi taho-mu-gamu da maharan Boko Haram daidai kusa da garin Auno, inda maharan su farmaki tawagar Sanata Sheriff da kimanin karfe 6:30 na yammacin ranar, yayin da gumurzun musayar wutar ya jawo mutuwar yan-sanda biyu, da mutum biyu da soja guda daya.
Majiyar ta kara da cewa, daya daga cikin motoci taran da ke tawagar ta yi kwatsa-kwatsa a garin Auno a sa’ilin da jami’an tsaron musamman da ke yaki da ta’addanci wadanda aka kirke a kauyen Njimtilo su ka kai zazzafan martani ga maharan. Tirnatsatsin da ya tilasta maharan ja da baya.
Advertisement

labarai