Wasu mahara da a ke kyautata zaton Boko Haram ne sun kashe mutane biyar tare da sace wasu fararen hula masu yawa a lokacin da suka kai farmaki a wani kauyan da ke kusa da garin Chibok, ta karamar hukumar Chibok, a Jihar Borno, a kwana guda da bikin ranar Kirsimati, kamar yanda rahotannin ‘yan banga da mazauna wajen suka nuna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Talata, a kauyan Korogelem, da ke da nisan kilomita 10 da garin Chibok.
Wasu majiyoyin sun ce ‘yan ta’addan sun sanya wuta a gidajen kauyan a bayan da suka kwashe kayayyaki masu amfani da kuma kayan abinci daga cikin su.
A cewar jami’an ‘yan bangan, ‘yan ta’addan sun ci karfin Sojojin da suke a kauyan ne na tsawon awanni a lokacin da fararen hula suka tsre daga kauyan domin neman tsira da rayukan su.
“Sun zo su da yawa ne, suna ta yin harbi ta ko’ina. Mun yi kokarin fafatawa da su, amma sai suka ci karfin mu saboda yawan su.
“Mun rasa mutane biyar a kauyan mu, kuma sun kwashe wasu ‘yan mata da manyan mata sun tafi da su. mun bincike duk dazukan da ke kusa amma har yanzun ba mu gansu ba. a yanzun haka muna zaman jimami ne sabili ma da ga bikin Kirsimati ya zo,” in ji ‘yan bangar.
Wani mazaunin kauyan mai suna, Musa Bitrus, ya shaida wa wakilinmu cewa, maharan sun kwashe dukkanin abincin da suka tanada domin shagalin Kirsimati sun tafi da shi.
“Mugayen mutane ne, sun sace dukkanin kajin da muka tanada domin bikin Kirsimati. Da yawan mu ma duk har sun yanka kajin na su kafin zuwan na su, amma duk sun kwashe sun gudu da su. ba su bar mana komai da za mu yi bikin Kirsimati da shi ba,” in ji Bitrus.