Boko Haram Ta Kashe Sama Da Farar Hula 27,000 Cikin Shekaru 10 – Majalisar Dinkin Duniya

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya dan Nijeriya Mista Edward Kallon ya ce kungiyar boko haram ta kashe sama da farar hula 27,000 tun daga 2009 da rikicin ya fara a Arewa maso gabas din kasar zuwa yanzu.
Kallon yayi wannan batun ne a lokacin da yake jawabi a taron bikin tunawa da shekaru 10 rikici a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a ofishin majalisar dinkin duniya dake Abuja ranar Laraba.
Da yake jawabi kan rikicin da ya shafe shekaru 10, Kallon ya ce, harin da aka kai Nganzai a karshen makon da ya gabata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, na daya daga cikin munanan hare hare da aka kai a cikin shekarun nan.
Ya ce, karuwar matsalar tsaro a cikin watannin da suka gabata ya sanya sama da mutum 130,000 barin gidajen su zuwa sansanin gadun hijira. ya kara da cewa harin da aka kai alamace da ke nuna cewa har yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro a jihohin borno, Yobe da Adamawa.

Exit mobile version