Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home JAKAR MAGORI

Boko Haram Ta Sake Jefa Maiduguri Cikin Duhu

by Sulaiman Ibrahim
March 29, 2021
in JAKAR MAGORI
1 min read
Kudin Fansa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa

 

Mayakan Boko Haram sun sake lalata wasu turakun wutar lantarki a Maiduguri babban birnin Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.

Hakan ya jefa da yawa daga cikin jama’ar birnin cikin duhu saboda turakun wutar lantarkin da mayakan suka lalata. Wannan dai ba shi ne karon farko da mayakan suke lalata wadannan kayan wutar ba.

A watan Janairu sun kai harin kan turakun wutar lantarki, lamarin da ya sa sai da aka kwashe kusan wata biyu ana aikin gyaran wutar.

Rahotanni sun ce kwana uku kenan da aka gyara wutar, wanda aikin ya gudana karkashin tsauraran matakan tsaro.

Yankin da a mayakan na Boko Haram suka lalata turakun wutar na da nisan kilomita 50 daga birnin na Maiduguri. Wannan lamari na faruwa ne, yayin da dakarun Nijeriya karkashin rundunar “Operation Lafiya Dole” ta ce ta kashe da yawa daga cikin mayakan kungiyar a yankin garin Chibok.

Rundundar sojin ta samu wannan nasara ce bayan wani kofar-rago da ta yi wa mayakan, wadanda bayanan sirri suka ce suna ta tserewa, saboda galaba da ake samu akan su. “Jaruman dakarunmu, sun yi musu kwantan-bauna, suka far musu da karfin gaske, suka kashe mayaka 9 yayin da wasu dama suka tsere da harbin bindiga a jikinsu.” Wata sanarwa da sojojin suka fitar dauke da sa hannun jami’in yada labarai Brigadier General Mohammed Yerima ta ce.

“Haka zalika mun yi nasarar kwato bindigar AK 47 guda takwas da harsashai da dama, kuma yanzu dakarunmu sun karbe ikon yankin.” Sanarwar ta kara da cewa. Wannan kwantan-bauna da dakarun Nijeriyan suka ce sun yi wa mayakan, ya faru ne a tsakanin Chibok zuwa Damboa.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

NDLEA Ta Cafke Tsohon Da Yake Kai Wa ’Yan Bindiga Miyagun Kwayoyi

Next Post

Ku Ba Mu Kudi Ko Mu Yi Garkuwa Da Ku, Cewar Wasu Masu Damfara

RelatedPosts

Wiwi

NDLEA Ta Cafke Masu Fataucin Mutane Da Kwayoyi Na Naira Miliyan 564 A Abuja

by Muhammad
2 weeks ago
0

Babafemi ya ce wanda ake zargin mai shekaru 40 da...

kama

Yadda Danuwana Ya Tilasta Min Aikata Miyagun Laifuka –Wanda Ake Zargi

by Muhammad
2 weeks ago
0

A ranar Litinin Rundunar yan sandan karkashin jagorancin DCP Abbaa...

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

by Muhammad
2 weeks ago
0

Likitoci a Iraki sun bayar da rahoton haihuwar wani jariri...

Next Post

Ku Ba Mu Kudi Ko Mu Yi Garkuwa Da Ku, Cewar Wasu Masu Damfara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version