Connect with us

NAZARI

Boko Haram: UN Za Ta Tallafa Wa Mutum Miliyan 6 A Arewa Maso-gabas

Published

on

Majalisar dunkin duniya (UN) ta sha alwashin tallafa wa mutane sama miliyan 6 (6.1m); wadanda rikicin Boko Haram ya tagayyara, a yankin arewa maso-gabashin Nijeriya, nan da karshen shekarar 2018.
Babban jami’in majalisar, mai kula da ayyukan jinkai (Coordinator), a Nijeriya, Mista Edward Kallon, shi ne ya bayyana hakan, a wani babban taron da ta shirya a birnin New York, na Amurika, wanda aka yiwa lakabi da: Hada hannu wuri guda wajen lalubo hanyoyin karfafa mazauna gabar tafkin Chadi, ta ayyukan jinkai.
Kallon ya ce, “Har yanzu a Nijeriya, muna fuskantar kalubale fiye da sauran yankunan duniya. Saboda idan an yi la’akari da alkaluman da suka nuna kan cewa, kimanin mutum miliyan 10.2 ne matsalar tsaro ta shafa a arewa maso-gabashin Nijeriya, kuma akallah mutane miliyan 7.7 suna cikin bukatar agajin gaggawa”.
“Bisa ga hakan ne ma ya sa, muka shirya cewa ayyukan mu na jinkai, na wannan shekara ta 2018, zasu kunshi bayar da tallafin ga mutane 6.1, wanda muke sa ran aikin zai lakume biliyoyin daloli, a wannan shekara ta 2018”.
“Wanda kafin watan Oktoba na 2016, gwamnatin Nijeriya tare da hadin gwiwar kasashen duniya, sun yi hasashen aikin jinkan zai shafi mutum 395,000, a cikin mutane miliyan takwas (8) da wannan rikicin ya shafa”.
“Kuma ta hanyar gagarumin goyon baya da muke samu daga gwamnatin Nijeriya, ayyukan mu na jinkai sun kai ga mutane sama da miliyan 5.6, a shekarar 2017”.
“Kuma muhimmancin abin bai tsaya kan wannan adadi ba kawai, war wa yau, mun yi nasarar dakile matsalar karancin abinci, tare da tunkarar babban kalubalen barkewar cutar kwalara wanda muka hadu dashi, da na yan gudun hijira a yankin”.
Jami’in majalisar dunkin duniyar, ya bayyana cewa sun dauki matakin bayar da jinkai ga yan gudun hijira miliyan 1.7 a yankin, wanda ko shakka babu zai haskaka rayuwar al’ummar, bayan dogon lokacin da suka dauka suna fama.
Ya ce, halin da ake ciki yanzu wasu daga cikin wadannan yankunan babu wata matsala, inda mutane ke ci gaba da komawa garuruwan su. Ya kara da cewa, daga shekarar 2015 zuwa yau, mutane sama da miliyan 1.4 ne suka koma yankunan da aka samu zaman lafiya a yankin.
Mista Kallon ya bayyana damuwar sa dangane da halin da yan gudun hijirar da suka koma garuruwan su ke fuskanta, wanda hakan na iya sake jefa su cikin wata sabuwar damuwa, a burin su na farfadowa daga halin da suka tsinci kai; na karancin abubuwan more rayuwa, wanda ya nemi basu kungiyoyi jinkai da su tallafa.
Majalisar dunkin duniya ta ce, “Mun yi kira, wanda muka aiwatar dashi ta tsarin nan na Oslo-1 tare da hadi da na manufar kwamitin tsaro na Majalisar Dunkin Duniya, da ya nuna cewa akwai bukatar yiwa tufkar wannan matsala hanci”.
“Kuma ba zai yiwu mu tunkari wannan matsalar da ayyukan jikai kawai ba. Dole ne mu nemo tushen da ya rura wadannan matsalolin, wanda ciyar da yankin arewa maso-bashin Nijeriya, yana daga ciki”.
“Muna ci gaba da mayar da hankalin mu sosai kan tattauna matsalar talauci, wanda a dabi’ance ya kunshi fuskoki da dama, wanda yana daga cikin abinda muka yi la’akari dashi a yan kwanakin nan”.
“Mun kula da yadda matsalar canjin-yanayi ta taka muhimmiyar rawa wajen haifar da sakamakon matsalar. Wanda yunwa da rikici ke dadidiyar junan su; a matsayin kanwa uwar gami, a tashin-tashinar da ke yiwa wannan yanki na Tafkin Chadi barazana”.
Bugu da kari kuma, ya shaidar da cewa, babu zaman lafiya matukar ba ci gaba, kuma babu ci gaba matukar aka ce babu zama lafiya, sannan babu yadda za a yi zaman lafiya da ci gaba su samu gindin zama matukar babu kwakkwaran ginshikai (institutions).
Haka zalika kuma, Mista Kallon ya bayyana wa kungiyoyin jinkai kan cewa, kan cewa dole su yi hobbasa wajen kawo daukin gaggawa, domin ceton rayuka, ta hanyar samar da tsare-tsare masu ma’ana, da zasu gina rayuwar jama’ar da wannan matsalar ta shafa, inda bisani ita ma gwamnati za ta kawo nata dauki, da nauyin da ya hau kan ta.
“Wanda wakilin Nijeriya ya yi bayani dangane da shirin gwamnatin shugaba Buhari, wanda ka iya zama ginshiki a ci gaba tare da farfado da samun dorewar zaman lafiyar yankin- da yake gudana ta hanyar amfani da bangarorin da suka kamata; kamar majalisar dunkin duniya da Bankin duniya hadi da sauran kungiyoyin bayar da tallafin jinkai tare da gwamnati.
“Yayin da aka bukaci samar da kimanin dala biliyan 6.7 wajen tabbacin samun dawamamen zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso-gabashin Nijeriya, wanda kuma da dama daga cikin manyan cibiyoyin kudi na kasa da kasa sun fara gudanar da muradin”.
“Mun riga mun fara dora tubalin harsashen lalubo mafita a wannan rikicin wanda ya daidaita arewa maso-gabas, da zai sahale zaman lafiya mai dorewa, wanda kuma akwai bukatar amfani da hanyoyin siyasa a ciki”. Inji Kallon.
Mahalarta wannan babban taro, sun kunshi ko’odinetocin ayyukan bayar da jinkai, daga kasashen Nijeriya, Chadi da Kamaru, hadi da kungiyoyin bayar da tallafi daga gwamnatocin kasashen Norway, Burtaniya, Canada, Tarayyar Turai (EU), da Netherlands tare da kasar Amurika, a matsayin manyan kasashe masu bayar da agaji.
Wanda suka yi bitar muhimmancin takwaran wannan taron wanda aka gudanar a birnin Berlin; ran 3 zuwa 4 ga watan Satumba, da makamancin sa: taron Oslo na 2, kan yadda za a tunkari matsalolin da rikicin yankin Tafkin Chadi zai haifar, ba abinda ya jawo rikin ba kadai.
Advertisement

labarai