Boko Haram: Zulum Da Sanatocin Borno Sun Ziyarci Shugabanin Sojoji A Abuja  

Zulum

Daga Muhammad Maitela,

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno tare da rakiyar Sanatoci da ke wakiltar jihar a zauren majalisar kasa sun ziyarci babban hafsan hafsoshin soja, Janar Lucky Irabor, da shugaban sojojin Nijeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a Abuja.

 

Kakkarfar tawagar ta kunshi Gwamna Zulum, Sanata Kashim Shettima,  Sanata Mohammed Ali Ndume, Sanata Abubakar Kyari, hadi da shugaban jam’iyyar APC na riko a jihar Borno, Alhaji Ali Dalori, sun gana da shugabanin sojojin dangane da hare-haren Boko Haram da ake ci gaba da fuskanta a jihar.

 

Kafin su gudanar da tattaunawar sirri, Gwamna Zulum ya ziyarci ofishin shugaban rundunar sojoji, inda ya yaba masa dangane da kokari tare da sadaukarwar da sojojin ke nuna wa a fagen fama domin ganin an samu dawamamen zaman lafiya a jihar Borno.

 

Haka zalika kuma, Gwamnan ya bukaci sojojin Nijeriya su yi kokarin bunkasa alaka tsakanin yan kasa tare da gwamnati don samun nasarar yakin da ake ciki na matsalar tsaro.

 

“Saboda haka dole muyi duk abinda ya dace wajen inganta kyakkyawar alaka tsakanin yan Nijeriya, gwamnatin da sojoji. Akwai bukatar aiki wuri guda don samun nasarar yakin da ake da matsalar tsaro, tare da bai wa al’umma komawa gidajen su domin ci gaba da gudanar da rayuwa kamar yadda suka saba. Kuma za mu bai wa sojoji dukan goyon bayan da suke bukata kuma zamu ci gaba da hakan, a kudurin da muke dashi na shawo kan wannan matsala ta tsaro cikin kankanen lokaci.” In ji Zulum.

 

A nashi bangaren, shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya yaba da irin kokarin da Gwamna Zulum yake wajen bai wa sojoji cikakken goyon baya tare da bayyana ziyarar a matsayin wadda ta zo a lokacin da ya dace.

 

“Bisa ga wannan, a kashin kaina ina mai yabo tare da bayyana godiya dangane da kokarin Gwamna Zulum ga sojojinmu a karkashin Lafiya Dole, musamman tallafin magunguna, kayan abinci da makamantan su. Sannan muna da cikakkiyar masaniya kan wannan goyon baya abin a yaba.”

 

A karshe Janar Attahiru ya bai wa tawagar Gwamnan tabbacin daukar sabon salon tunkarar yakin da suke da mayakan Boko Haram da takwarorinsu.

Exit mobile version