Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
A wata ziyarar aiki da Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai a karamar hukumar Bama ranar Talata, domin duba bukatu da yanayin ci gaban jama’ar yankin da matsalar tsaro ta daidaita, ya bayar da umurnin gina gidaje 500 a garin Nguro Soye, da ke Bama.
A hannu guda kuma, Zulum ya bayyana kudurin sake gyara gidajen jama’a sama da 1000 a garin, wadanda mayakan Boko Haram suka kona, domin bayar da damar sake tsugunar da yan gudun hijirar yankin.
A lokacin wannan ziyarar, Zulum ya fara da yada zango a fadar Shehun Bama, Mai-martaba Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi, inda ya bayyana makasudin ziyara a garin, wadda ta kunshi gano halin da makarantu a yankin suke ciki tare da shan alwashin aiki tukuru a matakin bunkasa harkar ilimi a kowane mataki, musamman ga kananan yara a fadin jihar Borno.
Haka zalika, Gwamnan ya bai wa Shehun Bama tabbaci dangane da bukatar da ya mika wa gwamnatin jihar na habaka ayyukan gona ga manoma a wannan damina mai zuwa.
Har wala yau kuma, nan take Zulum ya bayar da umurnin daukar matakan da suka dace a fannin harkokin noma a Bama saboda yadda ake samun karin yan gudun hijirar da suke dawowa gida wanda hakan zai taimaka gaya.