El-Zaharadeen Umar" />

Bola Ahmad Tunubu: Sarka Mai Rikicin Rikirkita Najeriya (I)

Bola Ahmed Tunubu an fi sanin shi a matsayin uba, ja gayya kuma jagoran tafiya jam’iyyar APC a Najeriya da kuma yankin arewa maso yamma watau yankin Yarabawa.
Baya bukatar doguwar gabatarwa a siyasar Najeriya, yana da tasirin gaske a yankin da ya fito, ya kwarai wajan kullawa da kuma warwarewa, shi ne mutumin da ya fitini Obasanjo ya hana shi zaman lafiya a siyasa tun a shekarun baya, ya hana kowa tasiri sai abinda yake so a siyasa za a yi.
Shi ne ya jagoranci haduwar jam’iyyun da suka samar da wanzuwar jam’iyyar APC wanda ta samu nasarar a zaben 2015, ana sauraran maganarsa, kamar yankan wuka, sannan an shaidai shi da cewa mutun mai son kansa akan kowace harka.
Haka kuma baya da wani mafarki da gurin da wuce ya zama shugaban kasa idan shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa, wannan yasa tuntuni ya fara sharar fage zama shugaban kasa a shekarar2023.
A wannan iskan mai kadawa, babu wata fitina ko matsala a Najeriya da ta wuce Bola Tunubu, yana jan zaransa yadda yake so, babu wanda isa ya nuna shi na yatsa, sai dai kuma yana hangen wasu a matsayin matsalar zamansa shugaban kasa anan gaba.
Tun lokacin da suka yi wata sa-in-sa da shugaban majalisar Dattawa ta Najeriya Bukola Saraki, Tunubu ya sanya shi gaba yake neman ganin bayanshi a siyasa har zuwa yanzu fadan bai kare ba, kuma ba a san ranar karewarsa ba.
Shima Bukola Sarakin ya nuna cewa ya san abinda yake idan ba haka ba da yanzu sai dai buzunsa, saboda Tunubu yasa shi gaba, kuma ana gani ba wanda ya ce don me, sai aka rika cewa gara haka, wai ya raina Buhari, daman ance maganin biri karan maguzawa to an hadu haduwar kuma bata yi kyau ba, domin tsohon bayaraba ya kusa dafa kasa.
Akan Bola Tunubu abubuwa da yawa sun tabbatar da cewa Buhari yana da sakaci da kauda kai, da kuma barin matsala ta zama babba sannan idan ya ga babu sarkin sai Allah ya tsoma bakinsa ko ya tsawata ko kuma neman yadda za a yi maganinta.
Bola Tunubu ya zama karfen kafa a jam’iyyar APC ya koma kamar wani dodo da ake jin tsoro, babu wanda ke iya yi masa magana idan ya yi ba daidai ba, wannan ya kara bashi damar jan zaransa yadda yake so a wannan gwamnati da talakawa suka yi ta bisa kyakkyawan zaton wani ba zai zama rijiya ta bada guga ya hana ba.
Rawar da yake takawa a siyasar Najeriya ta tsoma mafi yawan ‘yan Najeriya cikin matsala, amma saboda wasu dalilai ko dai na siyasa ko kuma na san rai, sai a kauda kai a dora laifin a inda ba muhallinsa ba.
Bola Ahmed Tunubu shi ne ya hana majalisun Najeriya na wakillai da na dattawa zaman lafiya, wannan dalilin yasa suka kullaci bangaran zartarwa saboda sun kasa tsawatawa Tunubu, wannan yasa abubuwa suke tafiyar hawainiya a cikin mulkin Buhari, wannan yasa har gobe ake kallon–kallon tsakanin bangaran zartarwa da kuma bangaran majalisu.
Sakamakon wuce gona da iri da Bola Tunubu yake yi wa siyasar Najeriya, yasa shugabancin majalisun guda biya ya koma karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, sakamakon shu’amanci Tunubu yasa arewa aka barta a baya wajen more roman dimokoradiya a Najeriya.
Bola Tunubu ne mutun kwara daya da baya da mukamin gwamnati amma yana iya ba shugaban ‘yan sanda Najeriya umarni a aikata ba daidai ba, amma kuma Buhari kamar an yi masa asiri idan ya tanka dutsi ma ya yi magana.
Shigar shantun kadangare da Tunubu ke yi wa Buhari ta tabbatar da cewa fadan kwankwaso da Ganduje wanda yanzu haka ana sa ran cewa jam’iyyar PDP na iya yin nasara a gaban kotu wanda karara ta tabbata cewa fadar shugaban kasa ke ruru wutar rikicin, ta hanyar goyan bayan Ganduje, kulba na barna ana cewa jaba ce…
Masana harkokin siyasar Najeriya sun sha fada cewa duk wanda yake gwamna a jiharsa shi ne wuka shi ne nama, wannan kuwa babu wanda ke musun haka, dalili ke nan yasa aka ce dole Sanata Rabi’u Kwankwaso da Sanata Kabiru Gaya su yi biyayya ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje saboda shi ne shugaba a jiha.
Jama’a da dama sun rika ganin laifin Kwankwaso saboda kin biyaya ga shugabancin Ganduje wanda hakan ya taimaka wajan juyawa Kwankwaso baya a yakin da yake da Gwamna Ganduje, kuma Gandujen yana samun goyan bayan fadar shugaban kasa.
Lokacin da Sanata Aliyu Magatarkadar Wammako ya shirya zuwa Sakwato domin nuna kwarin kashinsa sakamakon komawar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, abin mamaki sai ga Wammako ya shiga Sakwato ya yi rangadi cikin nasara jami’an tsaro suna ba shi kariya.
Amma a jihar Kano abin ba haka ya kasance ba, duk lokacin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi yunkurin zuwa Kano, sai ka ji jami’an tsaro suna yi masa kashedi tare da gindaya masa sharuda da suka shafi harkokin tsaro.
Bayyanai sun tabbatar da cewa Bola Tunubu ne kanwa uwar gamin abinda ya faru a zaban Kano, shi kadai ya yi ruwa ya yi tsaki wajan ganin ya ci mutuncin mutanen Kano da kuma karyata shugaba Buhari na ikirarin da ya yi cewa ba zai amince da yin magudi ko amfani da ‘yan daba ba, amma abinda ya faru ya nuna cewa Tunbu ya kai kwallon dan…
Saboda mafarkinsa na zama shugaban kasa kuma yana hangen idan suka rasa jihar Kano kamar an samu nukusani game da zaban 2023, yasa aka yi abinda akayi, sai dai kila nan gaba gaskiya ta yi halinta, amma dai maganar gaskiya ita ce Tunubu ya zama nakiyar kan kashi ko anke sai an ci da ita.
Zaban Kano kaiwa idan aka dorashi akan sikeli, ya kamata a ce shugaba Buhari ya sauka daga kan mulki, duk da cewa Buhari ya zama abinda ya zama, amma wadanda suka iya tafiyar da shugabanci sun nuna cewa Buhari hotone kawai amma su Tunubu sun riga sun rikirkita Najeriya kuma suna sauraran ya gama wa’adin mulkinsa ya mika masa. Kan uba!
Idan ba a Najeriya ba a ina ne mutun irin Bola Tunubu zai nuna zababban dan majalisa ya ce ko dai ka bi abinda na zaba wato Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar Dattawan Najeriya ko kuma ka bar jam’iyyar APC, jama’a da dama sun yi imanin cewa ko shugaba Buhari ba zai fadi haka ba, domin yasan mutunci da kimar ‘yan majalisa.
Haka kuma jama’a da dama sun zura ido wajan ganin yadda gwamnatin Najeriya zata yi da kamfanonin Bola Tunubu da yaki biyan haraji na biliyoyin kudi, amma muna ji muna ganin yadda ake yi wa masu karamin karfi idan irin haka ta rutsa da su.
Sannan idan Bola Tununu ya yi nasarar samun majalisar Dattawa da kuma ta wakilai tare da mataimakansa, to magana tare kare, ‘yan arewa sai sun zama ‘yan rakiya a wannan kasa kuma a wannan zangon mulki karo na biyu na shugaba Muhammadu Buhari sannan za a ga fushin ‘yan arewa wanda ba a taba gani ba idan Allah Ya kaimu zabe mai zuwa.
Ya isa misali duk da irin barazana da cika wuri da Bola yake yi a wannan gwamnati amma sai gashi an bar yankin yarabawa a baya wajan baiwa shugaba Buhari kuri’u, amma kullin ana ganin irin manyan ayyukan da ake jefawa a yankin na su saboda kawai kadda a batawa Tunubu rai a siyasar Najeriya.
Idan da ace shugaba Muhammadu Buhari yana son gaskiya yana kuma daukar mataki nan take idan aka yi ba daidai ba, da yanzu yasa an harbe Bola Tunubu sakamakon irin bakin jinin da ya shafawa gwamnatinsa ta hanyar yin amfani da kusanshinsa da Buhari yana baiwa shuwagabanin tsaro umarni su aikata ba dai dai ba.
Saboda haka ko shugaba Buhari ya sani ko bai sani Bola Tunubu ba mutumin arziki bane a siyasar Najeriya, babban mafarkin da yake kwana yana tashi da shi, shi ne, tunda anki ba shi mataimakin shugaban kasa, to yana nan a madakata yana jiran wa’adin mulkin shugaban Buhari ya kare a shekarar 2023 ya karbi ragamar shugabancin Najeriya. Allah Ya sawake. Amin .
A gefe guda kuma abubuwan da mafi yawan Najeriya suka yi imanin da shi, shine, yana da wahalar gaske shugaba Buhari ya mika ragamar shugabancin Najeria ga wannan mutumin da ya hana siyasa zaman lafiya. Wasu na ganin kwanton bauna Buhari ya yi masa, za a ga canji a wa’adin mulkinsa na biyu musamman akan Bola mutun mai son kansa.

Exit mobile version