Muhammad Maitela" />

Borno Za Ta Yi Hayar Ma’aikatan Jinya 150, Likitoci 19

Gwamnatin jihar Borno ta kudurci aniyar daukar matakin hayar ma’aikatan jinya hadi da likitoci domin cike gibin karancin jami’an kiwon lafiya a jihar.

 

Wannan furucin ya fito daga bakin Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, dakin taron gidan gwamnatin jihar (EDCO Chamber) da ke birnin Maiduguri, a sa’ilin da yake kaddamar da kwamitin kwararru wajen aikin kafa kwalejin koyar da daliban kiwon lafiya da asibitin koyarwa a jami’ar jihar Borno, wadda ta fara a 2016, domin fara gudanar da aikace-aikacen kiwon lafiya.

 

Wannan matakin ya zo ne biyo bayan samun amincewar kungiyar likitoci ta Nijeriya, reshen jihar Borno (Nigeria Medical Association) tare da sauran bangarori, wajen daukar matakin gaggawa a sashen kiwon lafiya.

 

Bugu da kari kuma, musamman a halin da ake fuskanta na annobar korona, wanda ya raunata fannin kiwon lafiya, al’amarin da ya jawo gwamnatin jihar fuskantar sa a kan kari.

 

“Saboda hakan, gwamnati ta bayar da umurnin daukar ma’aikatan jinya 150, likitoci 19 hadi da sake dawo da tsuffin ma’aikatan jinya da unguwan-zoma 133; kuma baki dayan wadannan tsuffin ma’aikatan da su ka yi ritayan daga asibitocin jihar Borno ne ko daga asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri, da ma wasu a waje wadanda za su iya bayar da gudmawan da ake da bukata duk za su iya neman aikin.” In ji Gwamna Zulum.

 

Har wala yau kuma, daga ciki har da kirkiro kwalejin koyar da ilimin likita da samar da asibitin koyarwa ta jami’ar jihar Borno da aka kafa a 2016.

 

Bugu da kari kuma, Zulum ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta fara gayyato tsuffin ma’aikatan jinyar da likitoci, sannan da karin wasu sabbi don rage gibin da ake dashi tsakanin adadin ma’aikatan kiwon lafiya; idan an kwatamta da majinyata da ake dasu a jihar, musamman yankunan karkara.

 

“Akwai karancin kwararrun jami’an kiwon lafiya da likitoci a jihar Borno, musamman a kananan hukumomi, wanda ana fuskantar kalubale sosai dangane da sha’anin kiwon lafiya. Amma matukar mun samar da wannan kwalejin tare da asibitin koyarwar, mu na kyautata zaton hakan zai taimaka wajen kara yawan ma’aikatan jinyar da kwararrun likitoci.” In ji shi.

 

“Saboda jama’a da dama su na da wannan burin a zukatan su, kuma za mu yi kokarin ganin mun taimaka mu su, ta wannan fannin, tare da ware isasshen kudin da za mu yi amfani da su wajen dauko hayar likitocin da ba su horo na musamman zuwa kasashen waje wanda zai basu damar gudanar da ayyukan su a tsanake, kuma da ba su dukan goyon bayan da su ke bukata.” Ya nanata.

Exit mobile version