A ranar 7 ga watan Janairu, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da takwaransa ministan harkokin wajen Botswana, Lemogang Kwape a birnin Gborone.
Wang Yi ya ce, kasar Botswana ta zama kasa ta 46 a nahiyar Afrika da ta amince da shiga hadin gwiwar shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Hadin gwiwar raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” zai kara zurfafa mu’amalar moriyar juna tsakanin kasashen biyu, zai taimaka wajen bunkasa cigaban samar da kayayyakin more rayuwar kasar Botswana, da samun cigaban zamani a kasar, kana zai kawo alheri da al’ummun kasashen biyu.
Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, da ministan harkokin wajen kasar Lemogang Kwape, sun ce rattaba hannu kan yarjejeniyar shawarar “Ziri daya da hanya daya” wani sabon matakin cigaba ne na bunkasa dangantakar dake tsakanin Botswana da kasar Sin, wanda zai samar da sabon kuzarin zurfafa dangantaka a tsakanin kasashen biyu.(Ahmad)
Shugaba Xi Ya Duba Shirye-shiryen Da Ake Yi Na Karbar Bakuncin Gasar Olympic Ta Birnin Beijing A 2022
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya duba shirye shiryen da...