A kwanakin baya ne, gwamnatin jihar Sao Paulo ta kasar Brazil da cibiyar nazarin harkokin likitanci ta Butantan suka shirya taron manema labarai cikin hadin gwiwa, inda suka sanar da kammala gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 ta CoronaVac da kamfanin fasahar halittu na Sinovac na kasar Sin ya gudanar kan mutane a mataki na uku.
Sakamakon ya nuna cewa, wannan allurar rigakafin cutar COVID-19 ta yi kyakkyawan tasiri kan wadanda aka yi yiwa, ba ta da wata illa.
Shugaban cibiyar Butantan Dimas Covas ya ce, gaba daya, an yi wa masu aikin sa kai allurar rigakafin sama da dubu 20, kuma, sakamakon ya nuna cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 ta CoronaVac ta kasance allura mafi tsaro a fadin duniya, ta kuma dace da bukatun hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO, a don haka cibiyarsa za ta gabatar da rokon yin rajista kan wannan allurar rigakafin cutar COVID-19 ta CoronaVac ga hukumar sa ido kan harkokin kiwon lafiyar kasar Brazil.
Jiya da safe, an kai allurar rigakafin cutar COVID-19 ta CoronaVac miliyan 5.5 daga kasar Sin zuwa jihar Sao Paulo. A mako mai zuwa kuma, za a kai Karin allurar miliyan 2 zuwa wannan jiha.
Shugaban ofishin kiwon lafiyar jihar Sao Paulo Jean Gorinchteyn ya ce, bisa shirin da aka tsara, za a fara yi wa al’ummomin jihar allurar rigakafin cutar COVID-19 daga ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2021. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)