Connect with us

LABARAI

BRC Za Ta Kirkiro Da Sabbin Shirye-Shirye Don Ilmantarwa

Published

on

Hukumar gudanarwa na gidan rediyo mallakin gwamnatin jihar Bauchi (BRC) za ta kirkiro da sabbin shirye-shiryen domin ci gaba da ilmantar da jama’a hadi da fadakar da su kan manufofin da gwamnatin jihar ta Bauchi ta sanya a gaba domin samun nasararsu.
Mai rikon mukamin Daraktan gudanarwa na gidan rediyon ta BRC, Alhaji Idris Usman Sambo shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke yaba wa gwamnatin jihar a bisa samar musu da na’urar rarraba hasken wutar lantarki domin inganta aikin jarida a gidan.
Alhaji Idris Sambo ya ce duk da yanayin da gidan rediyon ke ciki a halin yanzu, za su ci gaba da gudanar da aiyukansu bisa kwarewa da bin dokokin aiki domin tabbatar taimaka wa gwamnatin jihar don samun nasarar ciyar da jihar gaba.
Kamar yadda yake shaidawa, na’urar Jannareto da gwamnatin ta basu, zai kai ga taimaka wa na’urar watsa shirye-shirye wajen ganin sun ci gaba da ilmantar da jama’a da fadakar da su musamman kan aikace-aikacen da gwamnatin jihar ta sanya a gaba.
Shugaban BRC ya bayyana cewar wannan wani mataki ne na gwamna Muhammad Abubakar na ganin ya kyautata kafar sadarwa mallkin gwamnatinsa domin jin dadin jama’an jihar ta Bauchi.
Alhaji Idris Sambo ya kuma baiwa gwamnatin tabbacin gudanar da nagartaccen aiki domin jin dadi da walwalar jama’an jihar, yana mai shaida cewar da zarar aka rigaya aka sanya na’urar Jannaretan aiki zai kara kyautatuwa, a bisa haka ne ya gode wa gwamnatin jihar a bisa tallafin nata, yana mai shaida godiyarsa da shi da illahirin ma’aikatan kafar.
Daga bisani kuma ya jinjina wa kokarin shugaban Daraktoci na BRC, Alhaji Shehu Abubakar a bisa kokarinsa na tabbatar da samar da wannan tallafin ga kafar.
Da yake bayani kan kalubalen da yanzu haka suke jibge kuwa, ya shaida cewar suna fuskantar wasu matsalolin a cikin gidan don haka ya nemi gwamnatin jihar ta kara himma domin shawo kan matsalolin domin tabbatar da kyautata aiki a kowani lokaci.
Yana mai neman a shawo kan matsalolin da suke akwai hadi da neman tabbatar da jin dadin ma’aikata domin kara musu himma da kuzarin aiki.
Alhaji Idris Sambo ya kuma sanar da cewar an cimma matsayar za a samar da dakin watsa labarai wa kafar daidai da zamani domin kai aiki matakin kwarewa.
Shugaban ya kuma nemi hadin kai dukkanin ma’aikatan BRC musamman Daraktoci da masu aiki a sashin labarai da su hada hanu waje guda domin tabbatar da kai gidan rediyon mataki na gaba.
Idris Sambo dai kwana-kwanan ne ya amshi ragamar shugabancin gidan a hanun Hajiya Jummai Liman Bello biyo bayan kammala aiki da ta yi, inda kawo yanzu Malam Idris Sambo ya himmatu domin ganin ya kai kafar mataki na gaba don ci gaban jihar Bauchi, wannan ma duk na daga cikin yunkurinsa kamar yadda wasu ma’aikatan kafar suna shaida mana.
BRC dai babbar gidan rediyo ne wacce a shiyyar Arewa Maso Gabas ake gayar ji da ita, ta shafe shekaru da dama tana gudanar da aikinta a karkashin kulawar gwamnatin jihar ta Bauchi, sai dai a ‘yan shekarun nan tana fuskantar wasu matsaloli wanda hakan ma na daga cikin matakin kawo karshen matsalolin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: