BRICS Ta Bi Sahun Sassan Dake Neman Kawo Karshen Rikicin Isra’ila Da Palasdinu
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

BRICS Ta Bi Sahun Sassan Dake Neman Kawo Karshen Rikicin Isra’ila Da Palasdinu

byCGTN Hausa
2 years ago
BRICS

Da yammacin jiya ne shugabannin kungiyar BRICS suka kira taron musamman kan batun Palasdinu da Isra’ila. Wannan ganawa na zuwa ne bayan wani muhimmin taron ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi da kasar Sin ta jagoranta da nufin kawo karshen rikicin Israila da Palasdinu, ta yadda daga karshe za a kai ga tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A jawabin da ya gabatar yayin taron shugabannin na BRICS ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki, ya zama wajibi kasashen BRICS su nemi a tabbatar da adalci da zaman lafiya kan batun Palasdinu da Isra’ila.

  • Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila 
  • Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Uruguay

Abu mafi dacewa na kawo karshen rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa tsakanin Palasdinu da Isra’ila shi ne, aiwatar da shirin nan na “kafa kasashe biyu masu ’yancin cin gashin kai”, da dawo da halaltattun hakkokin Palasdinu da kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.

Shugaba Xi ya ce, idan har ba a warware matsalar bisa adalci ba, to, ba za a taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya ba.
Galibin shugabannin kungiyar da suka yi jawabi, sun bayyana bukatar mutunta yarjejeniyar tsagaida bude wuta da sassan biyu suka cimma, wadda za ta kai ga sakin wadanda sassan biyu ke rike da su.

Kan haka shugaba Xi ya gabatar da shawarwari 3, inda ya yi kira da a dakatar da bude wuta domin cimma zaman lafiya da tsaro mai dorewa. Kuma dukkan bangarori masu rikici su dakatar da bude wuta da duk wani nau’i na rikici da kai hari kan fararen hula, a saki fararen hular da ake tsare da su domin kaucewa karuwar asarar rayuka da wahalhalu, a tabbatar da isar da kayayyakin agaji ba tare da tangarda ba da fadada ayyukan agajin jin kai ga mutanen Gaza da dakatar da tilasta musu kaura da katse wuta da ruwa da mai da ake wa al’ummar Gaza a matsayin hukunci na gama gari.

Masana na kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai domin kaucewa tsanantar rikicin da bazuwar tasirinsa kan baki dayan yankin Gabas ta Tsakiya.

Baya ga wadannan muhimman taruka, shi ma babban sakataren MDD Anthony Guterres, ya bukaci da a kai zuciya nesa a mutunta dokoki da ka’idojin jin kai da bukatar kare rayukan fararen hula da kaucewa tsanantar rikici, ta yadda za a kai ga tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya. Wannan ya kara nuna muhimmancin wanzar da zaman lafiya a duniya maimakon yin fito na fito. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Labarin Rasuwar Janar CG Musa Ba Gaskiya Ba Ne – Rundunar Tsaron Nijeriya

Labarin Rasuwar Janar CG Musa Ba Gaskiya Ba Ne - Rundunar Tsaron Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version