An Buƙaci Gwamnatoci Da Su Ba Harkar Ilimi Fifiko A Yankin Arewa

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai fafatukar inganta rayuwar mata da matasa mai suna ‘Progressiɓe Women and Youth Support Initiatiɓe Bauchi’ ta yi kira da babban murya ga gwamnatoci da sauran ƙungiyoyi da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin bunƙasawa gami da samar da ingattaccen ilimi a Nijeriya musamman a yankin Arewacin Nijeriya da ke baya ta fuskacin ilimi da ma Nijeriyan baki ɗaya domin ganin an inganta sha’anin ilimi.

Har-wala-yau ƙungiyar ta bayyana cewar haɗa hanu domin taimaka wa sha’anin ilimin mata da koya musu sana’o’in dogaro da kai, haɗe da taimaka wa sha’anin ilimin yara marasa galihu ko kuma waɗanda iyayensu ba su da ƙarfin kaisu makaranta a matsayin gudunmawar da ake da matuƙar buƙatarsa musamman a Arewacin Nijeriya inda ƙungiyar ta yi kira da babban murya domin ganin an samu masu ci gaba da wannan sa’ayin.

Da yake jawabi a wajen a fadar Sarkin Dambam a ranar lahadin nan da ta gabata sa’ilin da suka kai tallafin kayan karatu wa ƙaramar hukumar, Sakataren ƙungiyar ‘PWYIB’ Barista Hussaini Suleiman Saraki ya fara ne da bayyana cewar sun kafa wannan ƙungiyar ne a watan Junairun 2017 da nufin taimaka wa mata, matasa, da kuma marasa galihu a faɗin jihar ta Bauchi ta fuskacin tallafa. Ya kuma ci gaba da bayyana manufarsu inda ya ce ƙungiyar ta fito da nufin kare sha’anin ilimin mata da na yara musamman a yankin Arewacin Nijeriya.

Barista Saraki ya kuma ƙara da cewa “da yawan mata a yankin Arewa ba su tafiya da ilimin zamani, kuma ilimin nan shi ne dai mafitar kowace al’umma, yanzu duniya ta ci gaba ta fuskacin ilimi amma mu an bar al’ummarmu a baya. Ta hanyar ilimin nan ne kuma za mu inganta rayuwarmu ya kuma taimakemu wajen gudanar da harƙoƙin rayuwarmu don haka ne muka tashi tsaye domin ganin an samu ilimi ya shiga kowace lungu musamman na yankunanmu”. In ji Sa

Saraki ya bayyana cewar wannan ƙungiyar tasu dai tana aiki a dukkanin ƙananan hukumomi 20 na jihar Bauchi domin taimaka wa wajen ganin sha’anin ilimi ya fita daga halin da ilimin ke ciki a halin yanzu.

A nata jawabin, Ko’odinatan ƙungiyar taimaka ta fuskacin inganta rayuwar mata da matasan, Hajiya Aishatu Jafar Bashir, ta bayyana cewar sun kasance a garin Damban ne domin fuskantar ƙalubalen da ke tattare da sha’anin ilimi a ƙaramar hukumar, da kuma ba da ɗauki daidai da ƙarfinsu, a cewar ita irin wannan tallafin zai rage yawan matsalolin da suke jibge.

Ta ce: “A wannan ƙaramar hukumar na Damban mun ga wani gida, a dukkanin yaran gidan yaro ɗaya ne muka gansa da yunufom da kayan makaranta zai je neman ilimi, sauran kuma ba su da kayan tafiya neman ilimi. Sannan muna son ganin an samu yanayin da kowani yaro zai je makaranta da abubuwan da ake buƙata kamar yanda sauran ‘yan uwansa suka je neman ilimi”. Ta shaida

“A bisa yanayin da muka gano a wannan ƙaramar hukumar gidaje da dama suna fama da ƙarancin yunifum ɗin yara na makaranta da kuma sauran kayyakin ilimi kamar littafai da abun rubutu. Wannan dalilin ne muka zaɓi wannan ƙaramar hukumar mu zo domin mu taimaka don ganin an samu nasarar haɓaka sha’anin illimi a jihar da ma ƙasa baki ɗaya”. In ji Aisha

Daga nan ne kuma sai ko’odinetan ta yi kira ga Sarkin garin da ya tabbatar da sanya ido domin ganin sauran yaran da basu halartar makaranta sun dukufa zuwa domin su ma su samu ilimin da ya dace.

Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar Hajiya Samira Ibrahim, ta shaida cewar ilimi zai samu nasarar daidaituwa a Nijeriya ne idan gwamnatoci da ƙungiyoyi suka haɗa hanu da juna domin ganin an shawo kan matsalar da sha’anin ilimi ke fuskanta musamman a yankin Arewacin Nijeriya “ina kira ga gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su haɗa hanu da juna domin fitar da sha’anin ilimi daga halin da yake ciki a Arewacin Nijeriya”.

A jawabinsa na jinjina, Sarkin garin na ƙaramar hukumar Dambam Alhaji Baba Muhammad, ya bayyana jinjinarsa da kuma godiyarsu ga ƙungiyar a bisa tallafin da suka kawo wa garinsa. Sai ya bayyana aniyarsa na ba da tasa gudunmawar domin inganta janibin ilimi.

Sarkin ya ce matuƙar babu ilimi to tabbas al’umma suna ciki hatsari, domin a cewarsa ilimi shi ne ja gaban komai. Ya bayyana cewar wannan gudunmawar tabbas zai zaburar da iyaye kan muhimmancin tura yaransu makaranta. Sarkin ya kuma tabbatar wa ƙungiyar cewar a nasa janibin zai yi duk mai iyuwa wajen ganin sha’anin ilimi a ɗaukaka a yakin Arewacin Nijeriya.

Ababen da ƙungiyar ‘Progressiɓe Women and Youth Support Initiatiɓe Bauchi’ dai ta kai ɗauki a ƙaramar hukumar sun haɗa da kayyakin karatu, yunufom, jakurkunan karatu, ababen rubutu da kuma littafan rubutu, inda suka raga ga yara marasa galihu da suke ƙaramar hukumar.

Exit mobile version