Tun daga lokacin da al’uumma suka fahimci gwamnatocin yau suna ware maƙudan kuɗaɗe domin bayar da tallafi ga ƙungiyoyi,daga lokaci zuwa lokaci sai ka ga ƙungiyoyi sai haɗa kansu suke da nufin samun tallafi daga gwamnatoci tarayya ko jiha ko kuma ƙananan hukumomi. Amma ƙungiyar haɗa kai da ake kira da turanci (Annur Multi-Purpose Corporatiɓe Society For Women And Youth Progressiɓe) da ke ƙaramar hukumar Zariya, ita ta sha bamban da sauran ƙungiyoyi. Shugabar ƙungiyar HAJIYA HAJARA SHEHU ta shaida wa wakilinmu BALARABE ABDULLAHI haka a zantawar da suka yi,jim kaɗan bayan sun kammala wani taro da suka yi a Zariya. Ga yadda hirarsu ta kasance da wakilinnamu:
Menene manufar kafa wannan ƙungiya?
Mun kafa wannan ƙungiyar ce ‘yan shekaru kaɗan da suka gabata a nan ƙaramar hukumar Zariya.mun sami rijista da gwamnatin jihar Kaduna da kuma ƙaramar hukumar Zariya,wannan rijsta da mu ka yi shi ya ba mu damar gudanar da ayyukan ƙungiyar kamar yadda tsarin kundin ƙungiyar ya tanada.
Kuma game da manufar ƙungiyarmu,to mun kafa wannan ƙungiya ce da ƙudurin tallafa wa mata da matasa maza da kuma mata a duk inda suke a ƙaramar hukumar Zariya da kuma wasu ƙananan hukumomi da suke maƙotaka da ƙaramar hukumar Zariya.Domin mun fahimci rashin sana’ar dogaro da kai musamman ga matasa shi ke sa su su shiga hanyoyin marasu kyau da aikata munanan ayyuka,kamar shaye-shaye da sauransu
Ke mace ce a matsayin shugabar ƙungiyar,ya na alamta mata ke nan suka fi yawa a ƙungiyar?
Lallai mata matasa da kuma maza matasa duk mambobin wannan ƙungiya ce,kuma duk abin da mu ke yi a tare mu ke yi.Wanda kuma duk wasu abubuwa da suka shafi ciyar da wannan ƙungiya gaba,ɗaukar bunu mu ke yi wa matsalolin,hakan da mu ke tafiya,zan iya cewar mun sami nasarori ma su yawan gaske,wanda duk ɗan wannan ƙungiya ya shaida.
Kuma mun fara tafuyar da wannan ƙungiya da mutum 155, amma yanzu da al’umma suka ga yadda mu ke samun nasarori,mu na da mambobi fiye da ɗari bakwai da suke sassan ƙaramar hukumar Zariya, ya yin da wasu mambobin sun fito daga ƙaramar hukumar sabon gari ne.Amma saboda mun kafa ƙungiyar domin tallafa wa mata da matasa maza da kuma mata ne,shi ya sa mu ke tafiya da wasu mambobin da suka zo daga ƙaramar hukumar Sabon gari.
Ku na koya wa mambobin ku sana’o’i ne?
A halin yanzu ba mu fara koya wa mambobinmu sana’o’i ba, domin matsalar da mu ka lura da ita it ace,bai dace ka koya wa mutum sana’a bayan ya kammala koyon sana’ar ka ba shi takardar kware wa kawai k ace ya je ya ci gaba yin sana’ar da ya koya. Kuma wannan matsala mu ka hango, mu ka rungumi ba da tallafin kuɗi ga mambobinmu bisa tsarin da ƙungiyarmu ta tsara.
Abin da mu ke yi shi ne sayar da hannun jari ga mambobinmu,Wato hannun jari mu ke sayarwa dai-dai ƙarfin mambobinmu,mu ka kuɗi ba tare da sanya ruwa a ciki ba.Kamar in mamba na son Naira dugu biyar,zai bayar da Naira ɗari biya in dubu goma yak e so,zai ba da naira dubu ɗaya,har dubu dubu ɗari biyu mu na ba mambobinmu.Kuma mu kan sa ido na ganin duk wanda muka ba shi bashi,lallai ya gudanar da jarin kamar yadda aka yi alƙawari kafin a bayar da bashin.
Zuwa yanzu mun ba mata kimanin 65 bashin kuɗi domin ci gaba da sana’o’in da suke yi a gidajensu,wato sana’o’in ƙule-ƙule da kuma ƙananan sana’o’in da mata ke yi.Bisa binciken da mu ke yi,babu wasu matsaloli da mu ka gani daga waɗanda mu k aba su jarin.Duk kuma wadda ko wanda ya sami jarin kuɗin sai bayan wata shida ya ke fara biyan bashin a dunƙule
Duk wanda aka ba shini jari,bayan ya cire gundarin bashin da aka danƙa ma sa,sai ya raba ribar zuwa gida uku,kashi biyu na wanda aka ba bashin ne,kashi ɗaya kuma zai dawo da shi ga uwar ƙungiya da ta bas hi wannan jari,to ka ji yadda mu ke tallafa wa mambobinmu da kuma yadda suke amfana da wannan ƙungiya.
Akwai ɗaga kara da ku ke yi wa waɗanda ku ka ba jari,domin ka da a yi amfani da jarin wajen yin anko ko kuma bikin dangi?
Ai babu shakka akwai ko matakan da mu ke ɗauka,domin a lokacin taron da mu ke yi mu kan yi wa’azi ga mambobinmu,musamman waɗanda aka bas u jari,da lallai su riƙe amanar alƙawarin da suka ɗauka na amfani da jarin wajen yin kasuwanci,ba aiwatar da abubuwan da ka faɗi ba.Wannan mataki da mu ke ɗauka ya na tallafa ma na kwarai da gaske,kuma ya na tallafa wa waɗanda mu ka su jarin su yi abin da ya dace da jarin da mu ka ba su,mu kan ce ma su su zama ma su tsoron Allah da yin gaskiya a lamurransu da kuma cika alƙawarin da aka yi da su.
A nan gaba za ku leƙa wasu ƙananan hukumomi domin ku tallafa wa mata da kuma matasa?
Babu shakka mun kammala wannan shirin,musamman za mu fara da ƙananan hukumomin Giwa da Soba da sauran ƙananan hukumomin da mu ke ganin ba za mu fuskanci wasu matsaloli ba
Wasu hanyoyi ku ke samun kuɗaɗen da ku ke dayar da jarin ga mabuƙata?
Ta hanyar da mu ke samun kuɗin da mu ke bayar da jarin shi ne wasu a cikinmu su ke bayar da kuɗaɗen domin a tallafa wa waɗanda ke buƙata,bbaya ga wannan hamya babu wata hanya da mu ke samun kuɗin,domin ba mu zuwa banki mu ci bashi domin mu aiwatar da abubuwan da mu ka sa a gaba.