BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 2
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 2

byNuhu Ubale Ibrahim
2 years ago
Buda

Gaggauta Buɗa-baki yana tabbatar da mutane a kan sunna. Akwai hadisai a kan haka:

1.  An karɓo hadisi daga Sahlu dan Sa’adu Allah Ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Al’ummata ba za ta gushe a kan sunnata ba, matuƙar ba ta jirkinta buɗa-bakinta zuwa fitowar taurari ba “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan yana azumi sai ya umarci wani mutum ya hau wani abu mai tudu ya ga rana ta faɗi, idan ta fadi sai ya yi buɗa-baki.  Hadisi ne ingantacce Ibnu Khumaima ne yabruwaito [#2061] da Ibnu Hibbãn [#3510] da Hãkim [#1584].

  • BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 3
  • SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1

2. An karɓo hadisi daga Anas dan Malik Allah Ya ƙara yarda a gare shi ya ce: “Ban taɓa ganin Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya yi sallar magriba ba (alhali yana azumi)  face sai ya yi buɗa-baki ko da kuwa da maƙwalwar ruwa ne “Hadisi ne ingantacce Ibnu Hibbãn [#3504] da Abu Ya’alã [#3792] da Ibnu Khuzaima [#2063] da Bazzãr [#7127].

Jinkirta ta buɗa-baki saɓa wa sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ne, kuma mutane ba za su gushe ba cikin alheri matuƙar suka aikata sunna. Duba Ibnu Dakikil Id; Ihkãmul Ahkãm [shafi na 419].

Kuma jirkinta buɗa-baki koyi ne da ahlulkitãbi, watau Yahudu da Nasara kamar yadda ya gabata a hadisi. A cikin Musulumi an samu waɗanda suke kwaikwayon Yahudu da Nasara wajen jinkirta buɗa-baki, ba sa gaggauta yinsa, waɗannan mutane su ne ‘yan Shi’a, kuma suna ƙudurce jinkirta shi, shi ne daidai. Waɗannan hadisai da aka ambata suna yi musu martani.

Jinkirta buɗa-baki alama ce ta ‘yan bidi’a. Duba as-San’ani; Subus Salam [2/221].

Imam as-Shãfi’i Allah ya yi masa rahama yana cewa: “Ina son gaggauta buɗa-baki, da ƙin jirkinta shi, kuma ina ƙyamar hakan ne ga wanda ya jinkirta shi da gangan kuma yake ganin haka shi ne abin da ya fi falala” Duba as-Shãfi’i; al-Ummu [2/106].

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta
Ilimi

Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta

October 6, 2025
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya
Ilimi

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

October 5, 2025
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet
Ilimi

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

October 4, 2025
Next Post
Ramadan: Sanata Abdulaziz Yari Zai Raba Tirela 358 Na Kayan Abinci A Jihar Zamfara

Ramadan: Sanata Yari Ya Buƙaci Musulmi Da Su Yi Wa Shugaba Tinubu Addu'a

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version