Daga Abba Ibrahim Gwale,
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da nadin tsohon gwamnan jihar legas Na mulkin soja, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA.
Kafin bashi wannan mukami, shine shugaban kwamitin yaki da miyagun kwayoyi da shugaba Buhari ya kafa a kwanakin baya.
Idan zaku iya tunawa Buba Marwa shine Wanda a lokacin yana gwamnan jihar Legas ya kirkiro hukumar ladabtarwa a jihar ta Legas wadda ta kawo karshen aikata miyagun laifuka a jihar.