Mohammed Bala Garba" />

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Sababbin Shugabannin ANA Reshen Jihar Kano Da Sauran Jihohin Najeriya

Bismillahir Rahamanir rahim!

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin sarki mai kowa mai komai, mai yadda yaso kan wanda yaso yayin da yaso a inda yaso ko ana so ko ba’a so. Tsira da Amincin da salati da Taslimi su kara tabbata ga fiyayen halitta cikamakin Annabawa da Manzanni. Da Alayensa tsarkaka da Sahabbansa da duk wadanda suka bisa da kyau da kyautatawa har izuwa ranar sakamako.

Da farko ina mika sakon taya murna ga sabbin shuwagabanninmu na ANA (Association of Nigerian Authors) reshen jihar Kano, sune kamar haka:

Shugaba    Zaharadeen Ibrahim Kallah

Mataimakiyar shugaba    Maimuna Idris Sani Beli

Magatakarda    Tijjani Muhammad Musa

Mataimakin magatarda    Sani Abba Sa’idu

Ma’aji    Bilkisu Yusuf Ali

Jami’in shige da ficen kudade    Danladi Zakariya Haruna

Jami’in hulda da jama’a bangaren Hausa    Abdullahi Lawan Kangala

Jami’in hulda da jama’a bangaren Turanci    Badamasi Aliyu Abdullahi

Jami’in walwala – Umma Suleiman ‘Yan Awaki

Lauya    Bello Sagir

Mai kididdigar kudade na  I    Yasser Kallah

Mai kididdigar kudade na II    Abba Shehu Musa

Tsofin mambobin na shugabanci

Hauwa Lawan Maiturare

Hassan Ibrahim Gama

Sadiya Garba Yakasai

Musa Ahmad Sunusi.

Muna muku fatan alheri da addur’ar Ubangiji Allah yayi riko da hannayenku ya baku ikon sauke nauyin dake kanku.

Naso halartar bikin rantsar daku da akayi domin bada wasu ‘yan shawarwari gareku da ma sauran shuwagabannin kungiyoyin marubuta na fadin Najeriya. Sai dai kash! Bikin yazo a dai-dai lokacin da nake kan jarrabawa, wannan yasa naga dacewar rubuto muku ‘yar wannan takardar domin baku wasu shawarwari.

Idan mukayi la’akari da abubuwan da ke afkuwa a harkar rubutu a wannan zamanin, zamuga sun yi kama da lamurran da suka kunno kai gabanin yakin duniya na farko. Idan ba’a dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya ba, “Tarihi zai iya maimaita kansa.” Kamar yadda masa iya magana ke fadi. 

Akwai wasu manyan kalubale dake gaban dukkan shuwagabannin marubuta ayau, wanda ya dace su maida hankali kansu don ceto harkar rubutu da marubuta a wannan zamanin. Wadannan kalubalen kuwa, sun hada da:

Rashin hadin kan Marubuta.

Ya da matukar mahimmanci musan cewa hadin kai babbar aba ce wanda ake bukatar duk wata al’umma ta kasance akai don cimma muradunta ba tare da samu wata tangarda ba. Idan kuwa haka ne, marubuta ne suka fi kyautatuwa ace sun siffantu da wannan sifar, saboda su suke rike da akalar al’umma. Idan kuwa suka rasa wannan sifar, to hakika zasu rasa wasu manyan muhimman abubuwa kamar haka:

1. Rashin karfi ta kowane bangare.

2. Rashin cimma muradunsu.

3. Rashin ci gaba ta kowani fanni.

4. Rashin kima da kwarjini da mutunci a idanun al’umma.

Babban matsalar data addabi harkar rubutu ayau shi ne rashin hadin kan marubuta. Wannan matsala ta rashin hadin kai kuwa, ta janyowa harkar rubutu da marubuta koma baya a wannan zamanin.

Wannan lamari na rashin hadin kai yana matukar cimin tuwo a kwarya, musamman idan na karanta mujalla ko jarida ko kuma na saurari radiyo ko talabiji idan ana hira da wani marubuci ko marubuciya, da an tambayesu babbar matsalar dake kawo musu koma baya sai kaji sun ce rashin hadin kai, wani lokacin ma kaji sun ce munafurci.

Shin wai dan Allah mai ya janyo wannan rashin hadin kan ko munafurcin? Kuma wani yunkuri aka taba yi domin magance wannan matsalar?

Zanso duk wani marubuci ko marubuciya su zauna suyi zurfin tunanin akan wannan matsalar domin gano hanyar da za a magance ta.

Da wannan nake kira ga dukkan shuwagabaninmu na kungiyoyin kamar su:

– Association of Nigerian Authors (ANA Kano)

– Mace Mutum Writers

– Hausa Writers Association of Nigerian (HAF)

– Katsina Writers Association of Nigeria

– Kainuwa Writers

– Raina Kama Writers

– Brigade Authors

– Nguru Writers Association of Nigeria

– Yobe Writers Association of Nigeria.

Da sauran kungiyoyin marubutan da bazasu lissafu ba, da su tashi tsaye haikan don magance wannan matsala ta rashin hadin kan marubuta, domin ita ce kadai hanyar da zata dawo da kima da darajar marubuta da rubutu a wannan zamanin. Allah yayi muku jagora, Amin.

Rashin bin ka’idojin rubutu:

Rashin bin ka’idojin rubutu na daya daga cikin babbar sillar karyewar tattalin arzikin rubutu a wannan zamani.

Ka’idojin rubutu kuwa, wasu dokoki ne da aka yi ittifakin yin amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa. Ita kuwa daidaitacciyar Hausa, daya ce daga cikin kare-karen harshen Hausa da aka zaba, aka daidaita mata ka’idojin nahawu domin yin amfani da ita cikin rubuce-rubuce da harkokin yada labarai a dukkan kasashen Hausa da ma duniya baki daya.

Aiki da ka’idojin rubutun yana matuka taimakawa wajen saukaka karatu, da gane abin da kai mai rubutu kake rubutawa, da fahimta daga su wadanda kake son isar wa da sakonnin garesu. Babban makama shi ne, sanin yadda ake harhada bakake a tada kalma. Hakan ya hada da sanin cewa idan ka hade kalmar da ya kamata ka raba za ta bayar da wata ma’anar ta daban da ba ita kake nufi ba. Rashin bin wannan ka’ida ta rubutu kuwa, ita tayi sanadiyar rashin ci gaban marubuta bila-adadin a wannan zamanin. Zaka samu marubuci ko marubuciya mai zalakar rubutu da kaifin basira, amma rashin sanin ka’idojin rubutu ko rashin bin ka’idojin yasa ko sunyi rubutun baza a fahimci sakon dake dauki a ciki ba. Sannan yana sa koda gasa marubuci ko marubuciya suka shiga anyi fatali da aikinsu, saboda rashin bin ka’idojin. Sai marubucin ko marubuciyar su dauka alkalan gasar ba kaunarsu suke ba.

Rashin bin ka’idojin rubutu babbar matsalar ce a duniyar rubutu, tama wuce babbar matsalar, mummunan aba ce mara kyawun gani da rashin dadin azanci. Rashin bin ka’idojin rubutu babban bala’I ne mai karya tattalin arzikin rubutu da marubutu.

Ina kira ga dukkan shuwagabannin kungiyoyin marubuta na wannan kasar, da su kirkiri wata doka da zata bada damar tantance rubuce – rubucen marubuta kamin ta basu lasisin bugawa su kai kasuwa. Allah ya datar damu, Amin.

Sanya Batsa cikin litattafanmu:

Yau an wayi gari Kalmar batsa ta zama tamkar wasali a cikin litattafanmu, musamman litattafan mata. Yana da mutukar muhimmanci musan cewa batsa haramun ce a dukkan addinan, sannan babbar bala’I ce dake karya tattalin arzikin rubutu.

Wannan matsalar ta batsa ta zama abin da ta zama musamman idan ka leka shafin yanar gizo na OKADA, inda zata tarar da litattafan batsa da ‘ya’yan musulmai suka zauna suka rubuta da hannayensu.

Yana daya daga cikin dalilan da yasa wasu iyayye ke haramtawa ‘ya’yansu karanta litattafan Hausa. Sannan ita tasa wasu jama’a ke kallon marubuta a matsayin mutanen dake bada babbar gudunmawa wajen gurbacewar tarbiyar ‘ya’ya, musamman tarbiyar ‘ya’ya mata.

Da wannan nake kira ga dukkan shuwagabannin marubuta musamman bangaren mata, da a dubi Allah a zauna a yiwa wannan tufkar hanci, domin akasari an san masuyi. Magance wannan matsalar zata taimaka wajen dawowa da marubuta martabarsu da kimarsu da darajarsu da mutuncinsu a idanun al’umma. Allah yasa mu dace, Amin.

Tallafawa kananan marubuta:

Kananan marubuta ayau sun zama tamkar ‘yan abi shata a sha kida, saboda rashin samun tallafi.

Ayau kananan marubuta na fuskantar babban barazana a harkar rubutu, saboda rashin karfinsu da kuma samun tallafin daga kungiyoyi da shuwagabanni.

Kananan marubuta sun zama ababen tausayi ayau, duba da dogaransu ga harka, ga kuma rashin karfi. Zaka samu marubuci ko marubuciya mai karfin basira da zalakar rubutu da sanin makamar rubutun, amma rashin  samun tallafi yasa su kare rayuwarsu cikin wahala ba tare da morar romon rubutu.

Da wannan nake kira ga dukkan shuwagabannin marubuta na fadin Najeriya, da su nemawa kananan marubuta tallafi koda daga gwamnatin jihohi ne, wanda zai taimaka musu wajen wallafe – wallafen litattafansu. Tallafin kuwa ba sai na kudi ba, koda gasa ce gwamnati ta rika saka musu duk shekara kamar yadda BBC Hausa ke sakawa marubuta mata.

Bayan gwamnati, akwai manya-manya kamfanoni da attajiri da sarakai masu kishin rubutu da bunkasarsa, ana iya neman tallafi daga garesu domin tallafawa kananan marubuta. Allah ya taimakemu baki daya, Amin.

Daga dan kankanin almajirinku, Muhammad Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

Wassalam.

Exit mobile version