Bude Makarantu: Gwamnati Na Son Ta Maida ‘Yan Nijeriya Zakaran Gwajin-dafi Ne Kawai –ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta sake jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da yin jinkirin sake bude makarantu a fadin kasar nan.

Kungiyar ta bayyana umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na sake budee makarantu a fadin kasar nan yayin da ake ci gaba da fama da annobar cutar Korona, zai iya jefa rayuwar dalibai cikin hatsari musamman talakawan daga cikinsu.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Bidoun Ogunyemi, ne ya bayyana hakan yayin ganawarshi da manema labarai na gidan Talabijin din Channels a jiya Laraba.

Ogunyemi ya ce, ‘Abinda gwamnatin ke kokarin yi a yanzu shi ne ganganci da rayuwar dalibai. Muna son yin gwaji ne da rayuwar ‘ya’yan talakawan kasa, wajen gano girman tasirin barnar da annobar korona za ta yi.’

Ya ci gaba da cewa; Yanzu gwamnati tana nufin a bude makarantu ba tare da an yi feshin magani ba a cikinsu? Gwamnatin da za ta iya yin feshin magani a kan hanyoyi da tinuna da kasuwanni.

Exit mobile version