Budurwa Mafi Tsawo Ta Yi Aure A Brazil 

Tsawo

A wani sanannen labari, wata budurwa mai shekaru 26 ta auri wani mutum mai shekaru 31. Ba abin mamaki bane auren, sai dai, tsawonsu ya sha bam-bam sosai, domin ta dara shi da kafa 2.

Rahotanni sun bayyana yadda suka hadu, suka yi aure duk da cewa ita Elisane Silba mai tsawo ce sama da shi mijin nata Francinaldo, kodayake ba a hukumance suka yi auren ba. Ita ce mace mafi tsayi a kasar Brazil, in ji rahoton Daily Mail. Budurwar da ta fito daga Salinopilis a kasar Brazil ta fara lura da saurin girmanta lokacin tana da shekaru 10.

A baya tsawonta ya kai kafa 5 da inci 9 to amma a yanzu ta kai kafa 6 da inci 8.

Budurwar mai shekaru 26 ta ce ta sha wahala ta fuskar zagi da izgili saboda tsayinta kuma sau da yawa ta kan kulle kanta domin ta nisanci jama’a, kamar yadda Metro.co.uk ta ruwaito.

Yadda ta fara soyayya da wani dan shekaru 31 Elisa daga baya ta yi aurenta tare da wani mutumi mai suna Francinaldo Da Silba Carbalho a cikin shekarar 2015.

A cewarta, sun hadu ne a shekarar 2011 kuma sun fada tsananin soyayya da kaunar juna. Gamayyar ta yi kyau, domin kuwa sun samu karuwar da Elisa ta yaba da gaskiyar cewa mijinta na son ta duk da bambancin tsawonsu kuma bai taba ganin hakan a matsayin matsala ba.

Ta ce: “Na ji wata alaka nan take a lokacin da na hadu da shi, kuma ban ma lura da tsayinsa ba. “Tsawon Francinaldo bai wuce kafa 5 da inci 4, wanda na dara shi da kafa kusan biyu, amma ban damu ba. “Duk da cewa yana sane da tsayina da yanayina, bai yi wasu munanan maganganu ba, kuma bai taba nuna damuwa ba.”

Exit mobile version