Budurwa Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Ya Je Saya Mata Shawarma A Kano
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Budurwa Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Ya Je Saya Mata Shawarma A Kano

byAbba Ibrahim Wada
3 years ago
Budurwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa mai suna Ilham Kabir Karaye da ake zarginta da sace motar saurayinta bayan da ya fita sayo mata Shawarma a unguwar Kofar Famfo, da ke kan titin Jami’ar Bayero a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar,  SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai da yammacin yau Litinin.

  • Dakataccen Malamin Kwaleji Ya Dawo Karen Mota A Ribas
  • Kasar Sin Za Ta Ba Da Gudummawar Dala Miliyan 50 Ga Asusun Yaki Da Annoba Na Bankin Duniya

A cewarsa sun samu rahoto daga wajen wanda aka dauke wa motar a ranar 12 ga Yulin 2022, inda ya kai korafin cewa an sace masa mota.

Bayan da ‘yan sandan suka kama ta, budurwar Ilham, ta bayyana cewa tana bin saurayin nata kudi ne N150,000 kuma tana ganin ba zai bata ba hakan yasa ta yanke shawarar dauke masa mota.

Sai dai a cewar saurayin, sun yi waya ne kuma suka hadu a hauren wanki, inda daga nan tace tana jin yunwa kuma shawarma take son ci, sai dai fitarsa ke da wuya domin siyo wa ya dawo ya tarar da motar ta yi batan-dabo.

Ilham dai ta bayyana wa ‘yan sanda cewa wani saurayinta ta kirawo ya tuka motar ya tafi da ita gida ya ajiye mata kuma ta dauki motar ne domin kudin da take bin sa.

Tuni dai aka kama Ilham da saurayin nata da ya tuka motar domin ci gaba da bincike.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Dokar Adaidaita Sahu A Kano: Za Mu Kama Duk Wanda Ya Karya Doka – ‘Yan Sanda  

Dokar Adaidaita Sahu A Kano: Za Mu Kama Duk Wanda Ya Karya Doka - 'Yan Sanda  

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version