Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Budurwa ‘Yar Ƙasa Da Shekara 20 Ta Lashe Gasar Hikayata Ta BBC Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere

Wata budurwa ‘yar ƙasa da shekara 20 da haiuwa, Aisha Musa Dalil daga Jihar Kaduna ta lashe Gasar Hikayata ta Sashen Hausa na Rediyon BBC, karo na shida.

Aisha wadda ‘yar asalin Jihar Adamawa ce ta fashe da kuka lokacin da take jawabin amincewa da lashe gasar da kuma godiya ga waɗanda suka shirya.
Sauran waɗanda suka zama gwaraza a gasar su ne: Aisha Hamisu Abdullahi daga ƙasar Nijer wacce ta zo ta biyu, sai kuma Zulaihat Alasan da ta zo ta uku.
Aisha Dalil dai ta yi zarra a gasar ce da labarinta mai taken “Hakkina”, wanda a ciki mijin mahaifiyar wata yarinya mai suna Fatima ya yi mata fyaɗe har ciki ya shiga. Yayin da wacce ta zo ta biyu kuma ta yi nasara da labarinta mai taken “Butulci” wanda ita ma wata yarinya mai suna Fatima ‘yar gidan mai hannu da shuni ta auri wani mayaudarin saurayi da ya haɗa ta da masu sace mutane suna garkuwa da su, don a tatse mahaifinta kuɗin fansa duk kuwa da halaccin da uban yarinyar ya yi masa na shatara ta arziki baya ga aura masa ɗiya. Ita kuwa Zulaihat Alasan ta yi nasara a gasar ce da labarinta mai taken “Adalci”. A cikin labarin ta kawo yadda wata mahaifiyar wani yaro da take ‘yar sanda ta jajirce wajen ganin an hukunta ɗan da ta haifa a cikinta wanda ya dawo karatu daga waje ya ɗirka wa mai aikin gidansu ciki. Sanadiyyar wannan tirka-rika dai uban yaron wanda shi ma ɗan sanda ne ya saki uwar saboda ta ƙi yarda a yi rufa-rufa kan lamarin.
Wacce ta zo ta ɗaya a gasar dai bayan takardar shahada da lambar yabo da aka miƙa ma ta, har ila yau an ba ta cakin Dalar Amurka 2000, yayin da ta biyu ita ma aka ba ta takardar shaida da lambar yabo da Dala 1000, kana ta uku ita ma aka ba ta takardar shahada da lambar yabo da kuma Dala 500.
Bayan tagomashin da gwarazan gasar suka samu, har ila yau Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya sanar da alƙawarin ci gaba da taimaka wa harkokin rayuwarsu har zuwa samun aiki a jihohinsu na asali ko jihohin da suke zama.
Da take jawabi kan yadda suka gudanar da aikin tantance masu gasar, shugaban alƙalan gasar ta bana, Dakta Hawwa’u Muhammad Bugaje, ta bayyana cewa, a cikin labaru 25 aka darje aka zaɓi guda uku don fitar da gwaraza.
Ta yi bayanin cewa gasar ta bana ta zo da labaru masu taɓa zuciya, domin ta yi ta sharɓar kuka yayin da take karanta wani, wani kuma ya sa ta cikin tsoro da firgicin halin da ake ciki a wannan zamani, a taƙaice dai har ramewa sai da ta yi a kan alƙalancin gasar saboda jigon labarun da ta karanta.
Ta yaba wa BBC Hausa saboda samar da kafar da take bai wa mata dama su amayo abubuwan da ke cunkushe a zukatansu, kana ta ce wannan namijin ƙoƙari da gidan rediyon ke yi zai ƙara inganta sha’anin zamantakewa a Afirka musamman a kan irin cin kashin da ake wa mata da kuma ƙara haɓaka Harshen Hausa.
Wakazalika, shi ma da yake jawabi, Shugaban BBC Hausa, Malam Aliyu Tanko, ya bayyana cewa “a kullum ƙoƙarinmu, mu fitar da abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma. A bana muna shekara ta shida da fara wannan gasa. Lokacin da aka fara, mata 200 suka shiga, amma a bana sun kai 500. Sannan ba ‘Yan Nijeriya ne kawai suka shiga gasar ba a bana, akwai wasu daga ƙasashe huɗu, Nijer, Kamaru, Sudan da Ghana. ɗaya daga cikin wacce ta yi nasara ‘yar Nijer ce. Don haka, wannan gasa ce ta ƙasar Hausa da Hausawa a duk inda suke a duniya.” In ji shi.
Ya yi fatan wannan nasara da ‘yan matan suka yi a gasar ta bana za ta zama silar inganta rayuwarsu. Kana ya geode wa duk baƙin da suka hallara a bikin karramawar.
Manyan baƙin da suka gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin da suka haɗa da Gwamna Badaru, Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Hafsat Ganduje, da Shugaban Hukumar Yaɗa Labaru ta Nijeriya, Alhaji Shehu Balarabe Illela da Shugaban Gidan Rediyon Nijeriya, Malam Mansur Liman, bakiɗaya sun jinjina wa BBC Hausa a kan wannan namijin ƙoƙari, tare da shan alwashin ci gaba da bayar da goyon bayansu ga muradun inganta rayuwar al’umma na gidan rediyon.

 

Exit mobile version