Buffon Ya Dawo Kungiyar Juventus

Tsohon mai tsaron ragar kasar Italiya Gianluigi Buffon ya koma Juventus bayan kammala kwantaraginsa na shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain.
Dan wasan mai shekaru 41, ya kwashe shekaru 17 a kungiyar kafin ya bar su a kakar wasan da ta wuce. Ya lashe kofin Siriya A sau tara sannan ya doka wasan karshe a gasar zakarun nahiyar turai sau uku.
Juventus ta bayyana a shafin cewa, ‘Barka da dawo wa gida Gigi. A ranar 19 ga watan Mayu na shekarar 2018 dukkan yan kungiyar da masoyan kungiyar suka yi kukan rabuwa da Gigi daga Juventus. Shahararan mai tsaron ragar ya lashe kofin duniya a 2006 sannan yafi kowanne dan wasa bugawa kasar Italiya wasa inda ya buga wasa 176. Ya koma PSG a karar wasan da ta wuce inda ya buga mata wasa 25 sannan ya lashe kofin Ligue 1
Exit mobile version