Connect with us

WASANNI

Buffon Ya Sake Kwantiragin Shekara Daya A Juventus

Published

on

Mai tsaron ragar qungiyar qwallon qafa ta Juventus, Gianluigi Buffon ya tsawaita zamansa zuwa kakar wasa daya a qungiyar da ke jan ragamar gasar Serie A ta bana bayan wata doguwar tattaunawa da dan wasan yayi da shugabannin qungiyar a kwanakin baya.

Tsohon mai tsaron ragar tawagar Italiya zai cika shekara 43 a lokacin da kwantiraginsa zai cika a Juventus a badi kuma yayi alqawarin zai ajiye takalmansa ne a qungiyar ta Juventus wadda anan ne ya qarar da shekarunsa na qwallon qafa a duniya.

Buffon ya sake komawa Juventus da tsaron raga a shekara ta 2019, bayan kakar wasa daya da ya yi a qungiyar qwallon qafa ta Paris St Germain wadda ta bayyana cewa ba zata iya ci gaba da riqe tsohon dan wasan qasar Italiyan ba.

Buffon ya buga wa Juventus wasannin Serie A sama da 500 tun lokacin da ya koma qungiyar a shekarar 2000 sannan ya kuma fara sana’ar qwallon qafa da kama raga a wasan farko a karawa da Parma a shekarar 1995.

Har ila yau, shima kyaftin din Juventus, Giorgio Chiellini ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara daya bayan da shima kwantiraginsa a qungiyar ya qare kuma shugabannin qungiyar suka buqaci ya ci gaba da zama saboda suna buqatarsa.

Juventus wacce take ta daya a kan teburin bana ta bayar da tazarar maki hudu a gasar Serie A tsakaninta da qungiyar qwallon qafa ta Inter Milan kuma saura wasanni 10 a qarqare kakar wasan shekarar nan.

Ita dai Juventus na fatan lashe kofin Serie A na bana kuma na tara a jere wanda hakan zai bata damar kafa tarihin lashe kofin rukuni-rukuni sau tara a jere wanda aka dade ba’ayi ba a manyan gasannin nahiyar turai a tarihi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: