Umar A Hunkuyi" />

Buhari Ba Zai Goyi Bayan Oshiomhole Kan Dakatar Da Ni Ba –Okorocha

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya nisanta shugaba Buhari daga abin da ya kira da rashin bin doka da yake zargin shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da aikatawa.
Okorocha, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ta hannun sakataren sa na yada labarai, Sam Onwuemeodo, ya ce Buhari tsarkakke ne a kan ya goyi bayan Oshiomhole, a kan wannan danyan aikin da ya aikata.
Gwamnan ya ce, Oshiomhole ya aikata abubuwa masu yawa da suka sabawa ka’ida a APC.
Okorocha ya kwatanta dakatarwar da aka yi ma shi da kuma gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, daga jam’iyyar ta APC da cewa, abin damuwa ne.
Wani sashe na sanarwar na cewa, “’Yan Nijeriya daga dukkanin sassan kasar nan ne suka zabi shugaban kasan, saboda ya tabbata shi mai gaskiya ne da za a iya aminta da shi. Da ya ce yana yakar cin hanci da rashawa, kowa ya ga yana aikata hakan. Ba zai zama kamar na wani da yake sayar da tikitin jam’iyyar ba ga masu kudi.
“Har yanzun ba mu ga wani dan Nijeriya a halin yanzun da zai iya doke shugaba Buhari ba a wajen zabe. Ya samawa kansa karbuwa a wajen yawancin ‘yan Nijeriya, a duk Jihohin da bai ci ba, kowa ya ga irin murdiyan da aka tafka a sakamakon zaben kamar misali na Jihar Imo.
“A takaice, ba ruwan shugaban kasan da abin da Oshiomhole ya aikata.”

Exit mobile version