Sabo Ahmad" />

Buhari: Ba Zan Manta Da ‘Yan Nijeriya Ba Lokacin Da Suke Cikin Tsanani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Nijiriya cewa, ba zai taba mantatawa da su ba, musamman lokacin da suke cikin tsanani, kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin ganin an samu dawwamammen zaman lafiya, a ko’ina da ke fadin kasar nan. Saboda haka ya ce gwamnati za ta ci gaba tallafawa ‘yan gudun hijira da kuma kokarin ganin kowa ya koma gidansa domin ci gaba da rayuwa kamar yadda sauran al’ummar ke yi.

Sakon da ya fito daga mataimakin daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Mista Attah Esa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Fadi hakan ne a Jiya Juma’a ta bakin babban mataimakinsa a kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, wanda shi ne ya karbi ‘yan gudun hijirar da suka kawo wa shugaban kasar ziyara a fadar ta Billa da ke Abuja.

A nan ne shugaban kasar ya taya ‘yan gudun hijirar guda 2,000 da suka yi sansani a Kuchingoro da ke babban birnin tarayya murna bisa nasarar da suka samu ta koma wa garuruwansu da ke Arewa maso gabas.

Haka kuma shugaban kasar ya yi godiya ta musammam ga kungiyoyin kasashen waje da kuma ‘yan Nijeriya musamman irin su Aliko Dangote, da Janar T.Y Danjuma da daukkan wadanda suka taimakawa ‘yan gudun hijirar ta kowace hanya.

Misis Maryam Nuhu, wadda ita ce shugabar ‘yan gudun hijirar wadanda ma fi yawansu mata ne da kananan yara ta yaba wa kokarin gwanmatin Muhammadu Buhari na cin galabar ‘yan kungiyar Boko Haram, wanda hakan ce ta sa yau suke shirin komawa gidajensu wadanda suka baro na tsawon lokaci.

“Yanzu haka mun samu tabbacin an fatattaki ‘yan kungiyar ta Boko Haram daga yankunanmu, saboda haka yanzu mun shirya tsaf domin komawa gidajenmu,” in ji ta. Saboda haka ta ce a madadain sauran ‘yan gudun hirar tana mika cikakkiyar godiya ga shugaban kasa bisa wannan kokari na sama musu ‘yanci da ya yi, na komawa muhallin da suka fito.

Exit mobile version