Akalla Atiku yana da bukatar yin jira na wasu shekaru uku, in dai yana nan da burinsa na mulkan Nijeriya. Wannan wasu bayanai ne kamar yanda kotun koli ta kasar nan ta zartar da hukunci a kai.
Kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Buhari ya samu a matsayin wanda ya lashe babban zaben shugaban kasa na shekarar zabe ta 2019, inda kotun ta yi watsi da daukaka karar da Atiku Abubakar ya yi na kalubalantar sakamakon zaben.
Ga ilahirin ‘yan Nijeriya wannan labarin yana nufin:
Buhari ne zai yi mulki har ya zuwa 2023
Hukuncin da kotun kolin ta yi na yin watsi da dukkanin hujjojin Atiku guda 66 da ya daukaka karan a kansu ya nuna, Buhari wanda haifaffen Jihar Katsina ne mai shekaru 76 a halin yanzun shi ne zai ci gaba da mulkar kasar nan har zuwa lokacin da za a sake yin wani zaben domin sanin wanda zai gaje shi a shekarar 2023.
Hukuncin duk da kotun koli ta zartas shi ne hukunci na karshe kamar yanda tsarin mulki ya ayyana a kan duk wata Magana ta zabe. (Hakan ya sanya Hausawa ske kiranta da, “kotun Allah Ya Isa).
Atiku wanda ya zo na biyu a zaben na ranar 23 ga watan Fabrairu da kuri’u milyan 11,262,978, ya jima ya musun cewa an tafka magudi ne a wajen zaben domin shugaban kasa mai ci a lokacin Shugaba Buhari wanda ya sami kuri’u milyan, 15,191,847.
Wasu daga cikin abin da Atikun ya nemi kotun da ta yi shi ne: ta yarda da cewa Buhari ya yi karya a karakashin rantsuwar da ya yi dangane da matakin iliminsa, na cewa takardar kammala karatun Sakandare ta shugaban kasan ‘yar jabu ce, sannan sakamakon da aka tatsa daga shafin yanar gizo na hukumar zaben ya nuna cewa dan takaran na Jam’iyyar ta PDP shi ne ya lashe zaben, sannan kuma yana son kotun ta amince da cewa hukumar zaben ta rika tura sakamakon zaben ta yanar gizo inda kuma hukumar zaben ta murda sakamkon zaben domin nasarar shugaba mai ci.
Watanni 8 a bayan zaben da kuma watanni 5 a bayan rantsar da Buhari a karo na biyu, a yanzun dai kotun kolin ta yi watsi da dukkanin abubuwan da Atikun ya nema da ta yi ma shi, tana mai cewa babu cikakken dalili a kansu.
Abu mai mahimmanci a kan wannan hukuncin shi ne sanin ‘yan Nijeriya dai suna nan tare da Buhari a matsayin shugabansu har na tsawon wasu shekaru uku.
“Tilas ne na amince da cewabin matakin shari’a da na dauka a matsayina na mabiyin tsarin Dimokuradiyya ya zo karshe,” in ji Atiku a cikin wata sanarwar da ya fitar. “Shin an yi hukunci na gaskiya ko ba a yi ba, wannan ya ragewa ;yan Nijeriya ne da su yi na su hukuncin,”
Atiku ba zai sake komowa ba.
Kila Atiku ya sake tsayawa takara a shkearar 2023
Atiku ba zai taba gajiwa ba da tsayawa takarar neman shugabancin Nijeriya, ko da kuwa sau nawa ne za a kayar da shi.
Haifaffen dan siyasar na Jihar Adamawa, ya fara neman ofishi mafi girma ne a kasar nan tun a shekarar 1992, inda yay i takarar neman shugabancin kasar nan a mataki na zaben fitar da gwani a cikin Jam’iyya a shekarar 2006, 2011, 2015 da 2019.
A lokacin da shekarar 2023 ta zo, Atiku zai kasance yana da shekaru 75 da haihuwa a Duniya kenan, kusan shekaru daya da shugaba Buhari a yanzun haka.
Akwai bukatar Jam’iyyar PDP ta kara turzawa a matsayinta na Jam’iyyar adawa
A daidai lokacin da wannan maganar ta kare, hanya mafi sauki ta gane ‘yan kura-kuran da suke a cikin karar ta Atiku da Jam’iyyarsa ta PDP.
Dukkanin maganar da ake yi ta bayyana sakamkon zabe ta hanyar yanar gizo da kuma batun murguda sakamakon zaben ya zama tamkar mafarki ne kadai. Domin alkalumman ma bas u yi daidai ba, lissafin ma ba ya daidaituwa.
Watanni da kasancewar Shugaba Buhari a karagar mulki, Jam’iyyar ta PDP ta gaza taka wata mahimmiyar rawa da ya yi kama da kasancewarta babbar Jam’iyyar adawa da za a iya rika a matsayin wacce za a iya bi.
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, da tawagarsa kamata ya yi su nuna adawar ta gaske fiye da abin da suke yi a halin yanzun.
Ba kasafai akan ji jam’iyyar adawar tana jan musu ba, yawancin sanarwowinta duk sukan rasa wata kima da madogara mai karfi, ta dai tsaya tana jiran wani lokacin zaben ne ya zo domin ta tunatar da ‘yan Nijeriya cewa tana nan fa.
Wannan duk bai yi kama da abin da ‘yan adawa a mulkin Dimokuradiyya suke yi ba a lokacin da ake kiran su da ‘yan adawa daruruwan shekaru da suka gabata.