Connect with us

RAHOTANNI

Buhari Da Ganduje Ba Su Da Na Biyu A 2019 (II) –Khalid Tudun Fulani

Published

on

Ci gaba daga jiya…
Ko akwai wani shiri na musamman da wannan kungiya take yi don ganin Buhari da Ganduje sun sake darewa kan kujerunsu a 2019?
Maganar da ake yi yanzu, tuni shirye-shirye sun yi nisa don kuwa tun daga kan Babban jami’in gudanarwa na wannan kungiya (Coordinator) da Daraktoci da sauran Shugabanni da kuma Mambobi, muna haduwa mu zauna a kowace rana ta Asabar din karshen mako don tattauna halin da jam’iyya ke ci da ita kanta gwamnati da kuma yadda za a magance ko warware matsaloli, idan kuma nasarori ne mu duba mu ga yadda za mu tallata su don sauran al’umma wadanda ba su sani ba, su sani.
Sannan mu a matakinmu na kungiya muna yin kokari irin namu don kuwa izuwa yanzu mun kirkiri shirye-shirye iri daban-daban ta inda muke shiga cikin al’umma muna tallata musu kyawawan ayyukan da gwamnatin tarayya da ta jiha ke yi, sannan muna sake jan hankalinsu, su fahimta su kuma sake rungumar wannan gwamnati mai albarka, sannan su fahimci cewa rasa wannan gwamnati ba karamar asara ba ce ga kafatanin al’ummar Nijeriya da ita kanta Jihar Kano baki daya. Don kuwa sabuwar gwamnati da za ta zo, ba lallai ba ne ta kalli wadancan ayyukan alherin da ake shimfidawa don dorawa a kai ba, shi yasa muke ta ci gaba da wayarwa al’umma kai don sake baiwa wadannan Shugabanni dama su kammala wadannan muhimman ayyuka da suka bijiro da su.
Haka nan akwai shiri da muke kan yi na fara shiga kafafen yada labarai tare da bibiyar mutane cikin gidajensu mu fada musu manufofin jam’iyya da na gwamnatinmu don sake sahale mata a karo na biyu da kuma cimma kudirorinta na magance matsalolin da suka addabi wannan kasa wadanda APC ta gada daga wajen gwamnatin da ta shude ta PDP.

Harkar kungiya na tattare da kalubale iri daban-daban, ko wannan kungiya taku ta hadu da irin wadannan kalubale?
Babu shakka akwai kalubale dama a kanmu daga lokacin da aka kafa wannan kungiya kawo yanzu. Kadan daga cikin kalubalen da muke fuskanta shi ne matsalar kudi, a matsayinmu na kungiya matsalolin da za mu iya magancewa ta fuskar abinda ya shafi kudi bai taka kara ya karya ba, duk da cewa ya zama wajibi na yabawa wasu daga cikin makarraban gwamnati kamar Gwamishinan yada labarai, Kwamared Muhammad Garba bisa gagarumar gudunmawar da yake ba mu don samun nasarar Shugaba Buhari da kuma Gwamna Khadimul Islam Dakta Abdullahi Ganduje. A halin yanzu ma akwai alkawarin da ya yi mana duk dai don ganin wannan kungiya da gwamnatocin biyu sun samu nasarar abubuwan alhairin da suka sanya gaba.
Akwai daya nasa takwaran, Hon. Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda tuni wannan kungiya ta ta tattaunawa da shi dangane da matsalolin kudi da sauran su da take fama da su, Daktan ya yi alkawarin ganin sai inda karfinsa ya kare don a cewarsa, dukkanin al’amarin da ya shafi Buhari da Ganduje ko kadan ba ya yin wasa da shi. Kazalika, akwai sauran Kwamishinoni da Manajan Daraktoci da Shugabannin kananan Hukumomi da sauran manya-manyan jami’an gwamnati da muka tattauna da su, suka kuma yi alkawarin tallafawa wannan kungiya tamu mai albarka.
Haka zalika akwai kuma mai gayya mai aiki, babban Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji wanda wannan kungiya ta yi tattaki ta kai masa ziyara Ofishinsa, ta gabatar masa da kanta da kuma matsalolinta, Allah cikin ikonSa, nan take ya karbe ta hannu biyu-biyu ya kuma yi alkawari cewa, a shirye yake wajen baiwa wannan kungiya dukkanin gudunmawar da take bukata don ci gabanta da na gwamnati da na kuma al’ummar Kano da Nijeriya baki daya. Muna sake yi wa Mai girma Sakataren Gwamnati godiya bisa mutunta mu da girmama mu da ya yi, Allah Ya saka masa da alheri, amin.

Akwai babban taro na jam’iyyarku da ke gabatowa, wane irin tsari ko shiri wannan kungiya taku ke yi don tunkararsa?
Tuni kungiyarmu ta gama nata shirin tsaf don tunkarar wannan taro da ake sa ran yin sa a ranar 26 ga wannan wata da muke ciki don sake zabar sabbin Shugabannin da za su ci gaba da rike ta. Alhamdulillahi, wannan kungiya ta kammala shirinta don mara wa Mai girma Gwamna da Shugaban Jam’iyya baya a wajen wannan babban taro da jam’iyyar ta shirya. A yanzu haka mu a kungiyance, mun tanadi motoci guda goma sha biyu duk da cewa a kowace karamar Hukuma cikin 44 da muke da su, muna bukatar akalla mota daya, haka nan a matakin jiha nan ma akwai bukatar akalla motoci hudu ko biyar. Motoci sha biyun nan da muka tanada, karo-karo muka yi a aljihunanmu, muna kuma bukatar karin wasu motocin kamar guda talati da uku zuwa talatin da biyar.
Babu shakka mun yi wannan tanadi ne saboda daukar wannan taro da muhimmanci da muka yi. Sannan muna kira ga sauran jami’an gwamnati da su zo su ba mu tasu gudunmawar don kuwa a wajen wannan taro ne muke son mu je mu nunawa duniya cewa, Mai girma Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne jagoranmu na APC a jihar Kano kuma cikakken zababben gwamna wanda ke tare da al’ummarsa, yake kuma yin aiki domin su. Kazalika, mun tanadi mutane akalla kimanin dubu daya da tari takwas don marawa Mai girma gwamnan baya.
Haka zalika, ina kira da babbar murya tun daga kan Mai girma Gwamna, babban Sakataren Gwamnati, Kwamishinoni, Shugabannin Kananan Hukumomi da sauran jami’an gwamnati da kuma Shugaban jam’iyya, dan Sarki jikan Sarki, Alhaji Abdullahi Abbas, da su taimakawa wannan kungiya da motoci, dakunan kwana ko masauki, kudaden da za mu baiwa ‘yan kungiya a hannu don cin abinci da abin sha da sauran su. Allah Ya bawa wadannan Shugabanni namu ikon taimakawa don ci gaban wannan kungiya da jam’iyya da Kano da kuma kasa baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: