Connect with us

LABARAI

Buhari Dalibina Ne A Siyasa –Bafarawa

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin Kasa a babban zaben 2019 a inuwar jam’iyyar PDP yana cewar kasar nan ta na fuskantar kalubale ne a bisa ga kasawar Muhammadu Buhari wajen gudanar da ingantaccen mulki.
Bafarawa ya ta’allaka dimbin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta a bisa ga rashin kwarewa da gogewar Buhari a fannin siyasa da sha’anin Gwamnati tare da tafiyar da salon mulki irin na mutum daya.
A tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan bayyana aniyarsa a karshen mako ya yi ikirarin cewar shi ne ya kawo Muhammadu Buhari a fagen siyasa.
“Siyasa aiki na ce domin ni dan siyasa ne tun daga matakin farko wanda ke fafutuka a cikinta a tsayin shekaru arba’in.”
Tsohon dan takarar Shugabancin Kasa na Jam’iyyar DPP a zaben 2007 ya bayyana cewar “Buhari dalibin siyasata ce domin ni na kawo shi a fagen siyasa kuma na bashi tikitin tsayawa takara a lokacin da nake shugaban rosasshiyar jam’iyyar ANPP na kasa don haka na san yadda zan gudanar da harkokin kasar nan da kuma jam’iyya.
Babban jogon na PDP ya bayyana cewar babbar matsalar kasar nan shine baiwa wadanda ba gogaggin ‘yan siyasa ba damar shugabancin al’umma a tsarin Dimokuradiyya.
Garkuwan na Sakkwato ya bayyana cewar wannan shine dalilin da yasa shugabanni ke nuna ko-oho ga manufofin jam’iyya yana cewar ‘yan Nijeriya na bukatar daidaitar al’amurra musamman a bisa ga yadda Gwamnatin APC ke tafiyar da al’amurran mulkin kasar nan.
Ya bayyana cewar ya yi jinkirin ayyana aniyar takara ne duk da yawaitar kiraye-kirayen da ake ta yi masa a fadin kasa bakidaya bisa ga yanayin kasa da na jam’iyyarsa.
Bafarawa ya bayyanawa magoya bayansa cewar ya aminta da tsayawa takara ne a bisa ga kaunar da yake yi wa al’ummar Jihar Sakkwato. A kan wannan ya bukace su da su hada kai a yi aiki tare duk da bambancin jam’iyya da ke akwai.
Tsohon Gwamnan ya bada tabbacin cewar jam’iyyar PDP za ta karbe mulki daga hannun APC a 2019, yana cewar jam’iyyar APC ta kasa cika alkawulan da ta yi wa ‘yan Nijeriya.
Ya ce wanda ya rike mukamin Gwamna, shugaban jam’iyya a matakin Karamar Hukuma zuwa Jiha zuwa Tarayya tare da lakantar fanni mai zaman kansa yana da cancantar da zai shugabanci kasar nan idan a ka bashi dama.
“Siyasar da nake yi ta ci-gaban jama’a ce. Jama’a a ciki da wajen Jihar Sakkwato sun bukaci in tsaya takara kuma ba zan ce a’a ba saboda burin da nake da shi na taimakon marasa galihu tare da gudanar da ayyuka masu tasiri, gina makarantu, asibitoci, hanyoyi, bunkasa aikin gona tare da karfafawa marasa galihu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: