Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ga Hafsoshin Tsaro: Kun Gaza A Aikinku

Published

on

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fusata game da yadda manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ke tunkarar yaki da masu tada kayar baya a kasar nan, yana mai cewa abinda suke yi bai taka kara ya karya ba ganin yadda ta’addanci ke kara samun gindin zama a kasar nan.

Mai ba shugaban kasa Shawara kan harkar tsaron kasar nan, Babagana Mongonu ya shaida wa manema Labarai a fadar gwamnati cewa shugaba Buhari ya ce ba zai sake sauraran su ba idan suka zo masa da wani abu ba nasara ba.

Ya gargade su da su maida hankali su je su yi aiki tukuru ko kuma ya dau mataki akan su.

Buhari yayi ganawa ta musamman ne da manyan hafsoshin tsaron kasar a fadar shugaban Kasa, yau Alhamis.

Advertisement

labarai