Daga Khalid Idris Doya
Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya aike da zazzafan gargadi ga ’yan bindigan da suke kai hari ga makarantun a fadin kasar, yana mai cewa ko da wasa Nijeriya ba za ta amince a tarwatsa mata tsarin makarantu ba.
Buharin a sanarwar manema labarai da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya jinjina wa kokarin gwamnatin jihar Kaduna bisa daukan matakan da suka dace domin ganin an ceto dalibai 180 ciki har da ma’aikata takwas, yana mai cewa sauran wadanda suka bace ma tabbas za su dawo cikin kwanciyar hankali zuwa ga iyalansu.
Buharin, ya kuma yaba da irin hadin guiwa da ake samu a tsakanin ‘yan tsaron sa-kai da suke cikin al’ummomi wadanda suke bada tasu gudunmawar wajen ganowa da zakulo masu garkuwa da mutane, yana mai cewa sanya idon jami’an sa-kai na cikin unguwanni da kauyuka na taimaka matuwa gaya wajen dakile aniyar bata gari.
Ya na mai cewa, duk da sojoji ke dauke da makaman tunkarar duk wata kalubalen tsaro, amma kuma suna matukar bukatar hadin kan jama’a da suke cikin kauyuka da unguwanni wajen ganin an taimaka musu da bayanan da suka dace domin hana ‘yan ta’adda cin karensu babu babbaka.
Har-ila-yau, shugaban ya kuma jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da bada tabbacin cewa gwamnati na kokarinta wajen ganin an samu saukin matsalolin tsaro da ake fama da su.
A wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari ya nemi da a koma amfani da tsohon tsari irin na da baya domin tabbatar da tsaro a kowani lungu da sako da shawo kan matsalolin tsaro da suke akwai a halin yanzu.
Buharin, yana mai cewa ta hakan, za a iya samun tagomashin shawo kan matsalolin da suke akwai na yawaitar aikace-aikacen ‘yan bindiga da hare-haren da suke kai wa jama’a babu gaira ko dalilin hakan.
Buharin yana mai kuma cewa ba zallar gwamnati ce ke da alhakin magance matsalar tsaro ba, kowa da kowa na da damar bada tasa gudunmawar musamman al’ummomi da suke cikin unguwanni da yankuna.
“Bayan na gama sakandare na shiga aikin soja, daga Laftanar zuwa Janar, na san a kowace karamar hukuma akwai majalisar tsaro karkashin Basaraken gargajiya da shugaban ‘yan sanda na yankin da baki makiyaya da ‘yan kasuwa.
“Akwai irin wannan majalisar (ta tsaro) a duk fadin kasar. Su na kai rahotonsu ne ga gwamnan jiha, sai dai idan akwai wani abu muhimmi sai a je wajen shugaban kasa.
“Ina umartar ku da ku gyara tsarin tsaro saboda a yi maganin matsalar a kowane mataki. Yanzu mun shantake, duk sanda wani abu ya faru sai mutum ya bazama zuwa fadar shugaban kasa.
“Kamar yadda na fada, za mu dirar wa masu aikata laifuka. Wajibi ne a dawo wa da mutane kwarin gwiwa a kan gwamnati a cikin mako shida masu zuwa, idan ba haka ba kuma za mu shiga cikin yunwa saboda manoma ba za su iya komawa gonakinsu ba.”