Buhari Na Bukatar Hadin Kan ’Yan Najeriya, Cewar Abuje Lokoja

Lokoja

Daga Ahmed Muhammed Danasabe

 

An yi kira ga yan Najeriya dasu baiwa shugaba Muhammadu Buhari cikakken hadin kai domin bashi kwarin gwiwar ciyar da kasar nan gaba.

Wani dan kasuwa da ke garin Lokoja, Alhaji Ibrahim Danjuma Abuje Lokoja ne yayi kiran a makon data gabata, a sa’ilin da yake amsa tambayoyin wakilin Jaridar LEADERSHIP A yau, a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Alhaji Ibrahim Abuje Lokoja yace babu yadda Shugaba Buhari zai samu nasarar kai Najeriya tudun na tsira ba tare da samun cikakken hadin kan yan kasa ba.

Dan kasuwan wanda ya shafe fiye da shekaru 25 yana harkar kasuwanci a garin Lokoja,ya bayyana cewa shugaba Buhari nada kyakkywan manufa ga kasar nan kuma an samu ci gaba ta fannoni da dama a tun lokacin da shugaban ya amshi ragamar shugabanci tun shekarar 2015 kawo a yanzu.

Alhaji Ibrahim Abuje ya zayyano fannin hasken wutan lantarki, harkokin noma, samar da ayyukan yi, samar da tsaro da kuma inganta tattalin arziki a matsayin wasu daga cikin muhimman nasarorin da shugaba Buhari ya samu a shekaru biyar ya jagorancin kasar nan.

Sai dai kuma dan kasuwan yayi kira ga gwamnonin kasar nan dasu rika taimakawa kokarin shugaban kasar na kai kasar nan da al’ummanta tudun na tsira, inda ya kara da cewa sai da hadin kan gwamnoni da kuma sauran yan kasa ne shugaba Buhari zai cimma buri da kuma kudurinsa na gina Najeriya.

Alhaji Ibrahim Abuje Lokoja wanda yace gwamnatin shugaba Buhari ta maido da martaba da kuma kimar kasar nan a idon duniya, ya kuma roki yan Najeriya, musamman matasa dasu bi hanyar diflomasiya wajen neman biyan bukatunsu a wajen gwamnati, ba wai sai sun shiga tarzoma da tada hankali ba.

Ya kuma shawarci matasa da kada su amince wasu marasa kishin kasa,su yi amfani dasu wajen tada zaune tsaye a kasar nan don cimma burinsu na son zuciya.

A karshe, Alhaji Ibrahim Abuje Lokoja yace yana da kyakkyawan fatan Najeriya zata kamo sauran takwarorinta da suka ci gaba irinsu Brazil,Indiya, Indonisiya da kuma sauran kasashe masu tasowa da suka samu ci gaba a fannin tattalin arziki.

 

Exit mobile version