Bello Hamza" />

Buhari Na Kokarin Cika Alkawarin Yakin Neman Zabensa, Cewar Minista

Minista

Ministan kimiyya da fasaha Dr Ogbonnaya Onu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari na aiki tukuru ba dare ba rana don ciki alkawarin yakin neman zabe da ya yi wa al’ummar Nijeriya wadanda suka gudanar da zabe.

Onu ya bayyana haka ne a garin Uburu ta karamar hukumar Ohaozara a jihar Ebonyi a yayin da yake tattaunawa da manea labarai bayan ya sabonta katin zama dan jam’iyyar APC da ake gudanawa a halin yanzu a fadin kasar nan.

Ministan ya gudanar da sabunta katin ne tare da matarsa Mrs Chinyere Onu da misaalin karfe 11 na safe  a Obiozara ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su yi tururuwa wajen shiga jam’iyyar APC don kuwa ita ce kadai za ta tabbatar da bunkasar Nijeriya da kuma kawo zaman lafiya a halin yanzu.

Exit mobile version