Abubakar Abba" />

Buhari Ne Mafita Ga Matsalolin Nijeriya, Inji Lai Mohammed

Daga  Abubakar Abba

 

Ministan yada Labarai da Aladu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewar idan shugaba  Muhammadu Buhari yaci gabada tafiyar da shugancin kasar, kasar zata ci gaba da kasance hannun da ya dace kuma wannan ba wani abin damuwa bane.

Lai ya sanar da hakan ne shekaran jiya lokacin da yake jawabinsa a wani karamin taron ganawa da ma’aikatan dake aiki na ofishin jakadanci na Nijeriya dake yankin Madrid a kasar Spaniya tare da kuma wasu ‘yan Nijeriya dake zama a kasar ta Spaniya.

Ministan ya ce, sabanin labarin kanzon Kuregen da wasu kafafen ‘yadawa a Nijeriya, kasar tana tafiya akan turba, musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasa da tabbatar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa, domin wadannan sune manyan shirye-shirye guda uku da gwamnatin shugaba Buhari ta mayar da hankali akai.

Acewar Ministan, ”kada ku amince da dukkan abinda kuka gani an wallafa a wasu kafar yada labarai ta yanar Gizo kuma Nijeriya bata fuskantar wani yanayi na yaki ko wani rikici.”

A wata sanarwa da mai taimakawa Ministan na musamman Segun Adeyemi ya fitar, Ministan yaci gaba da cewa, sabanin rahotannin da kake karantawa a kafar yanar Gizo, gwamnatin shugaba Buhari tana kokari wajen kafa kasar nan akan turba saboda tabargazar data riske.”

Ya bayyana cewar masu hana ruwa gudu suna ta faman kashe miliyoyin kudi don su zubar da mutuncin wannan gwamnatin.

Ministan  ya kara da cewa ya kamata a jinjinawa gwamnatin akan nasarorin data samu duk da kalubalen data riska a lokacin data dare karagar shugabancin kasar nan a ranar ashirin da tara ga watan Mayun shekarar 2015.

Ya yi nuni da cewa, an ce idan baka san daga inda kake tahuwa ba, ba zaka san inda kake tunkara ba kuma ya kamata  a san cewar kudin danyen mai ya fadii kasa warwas, inda kuma asusun kasar nan na kasar waje ya sauka zuwa dalar Amurka biliuyan ashirin da hudu, kuma akan maganar gaskiya, gwamnatin taryya tana ciwo bashi ne kafin ta biya ma’akatan ta kum amafi ywancin jihohi basa iya biyan albashin ma’aikatan su.

Ya bayyana cewar lokacin da wannan gwamnatin ta zo, kudaden fansho  da ba a biya ba a jihohi da dama sun kai biliyoyin naira ‘yan kwangila sun watsar da ayyukan da aka basu saboda suna bin basusssuka komai ya tabarbare samar da wutar lanatki ya tsaya akan megawatts 2,690  an kuma biya biliyoyin naira akan kudin tallafi na shigo da mafetur cin hanci da rashawa ya yiwa kasar nan a wancan lokacin daurin demo menti kuma kananan hukumomi ashrin zuwa ashirin da bakwai suna karkashin Boko Haram.

Ministan yace amma duk wadannna abubuwa a ayau sai tarihi, inda asusun ajiya na kasar waje a yau ya kai dalar Amurka arba’in da biyu da digo takwas wanda ya karu a cikin shekaru hudu kuma hauhawan farashin kaya ya ya sauka a cikin wata sha biyu zuwa kasha sha biyar da digo sha uku,inda hakan ya bai wa gwamnati damar ajiye  naira biliyan 108 a Banki tun kafin gwamnatin ta kirkiro da asusun ajiya na bai daya.

Ya ce, sakamakon samar da wannan asusun, kasar ta samu sukunin ajiye naira biliyan 24 a duk wata, kuma hakan ya kawar da ma”aikatan bogi nan ma gwamnati ta samu shigar naira biliyan dari da ashirin.

Ministan ya bayyana cewar sakamakon ci gaban da aka samu a harkar tattalin arzikin kasa, kudin shiga sun kai yawa dalar Amurka biliyan 1.8 a tsakiyar shekarar 2017, inda hakan ya linka zuwa dalar Amurka  miliyan  908 a farkon shekara a kasuwar hada-hadar kudi, idan hakan ya samarwa da kasar nan rara kasha arba’in bisa dari hakan kuma ya kara daga martabar Nijeriya zuwa ta ashirin da hudu wajen yin kasuwanci ta kuma zamo kasa  ta goma  mai farfadowa akan tattalin arzikin kasa.

Ya shaidawa mahalarta taron cewar Nijeriya tana kara matsawa gaba, musamman ta fannin noman shinkafar cikin gida kuma shirin ciyar da ‘yan makaranta da gwamnatin ta kirkiro dashi, ya samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, inda hakan ya samar da ayyukan yi ga masu dafa abinci har su 61,352, bugu da kari, shirin ana ciyar da yara ‘yan makaranta har miliyan shida da digo hudu dake jihohi ashirin na kasar nan.

Ministan ya bayyana cewar gwamnati ta kara yawan megawatts zuwa 7,000 kuma anci lagon ‘yan kungiyar haka gwamnatin tana ta kai Gwaro da Mari wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan. Ya yi kira ga ‘yan kasar nan dasu shiga yanar Gizo don kwafar shirin gwamnatin tarayya na (FGN-iAPP) don su samun sahihan bayanai daga Nijeriya don su amsa tambayoyi daga ‘yan kasar nan da suke son su sani ko ‘yan kasar nan dake zaune a kasashen waje za su iya yin zabe da yadda za su samu katin shedar dan kasa da kuma irin ayyukan da gwamntin take yi musammna don kawo karshen rikici a tsakanin manoma da makiyaya. Jakadan Nijeriya a kasar ta Spaniya, Susan Aderonke Folarin c eta jagoranci tawagar ma’aikatan zuwa taron wanda aka gudanar a harabar ofishin jakadanci.

 

 

 

 

 

Exit mobile version