Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Buhari Ya Amince Da Sake Bude Iyakokin Nijeriya Guda Hudu

by Khalid Idris Doya
December 17, 2020
in LABARAI
2 min read
Iyakokin Nijeriya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da sake bude iyakokin kasar nan guda hudu nan take ba tare da bata wani lokaci ba, a yayin da kuma ake sauraron bude wasu karin iyakokin nan kusa.

Ministan kudi da kasafi tare da tsare-tsaren tattalin arziki, Misis Zainab Ahmed, ita ce ta shaida hakan ga ‘yan jarida jim kadan bayan kammala ganawar mako-mako na FEC wanda ya gudana a jiya, ta na mai cewa har zuwa yanzu dai kuma ba a dage takunkumi kan shigo da wasu daga cikin kayayyaki ba irin su shinkafa da sauran ababen da ake sarrafawa.

samndaads

Ganawar wanda ya gudana ta kafar bidiyo, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranta, inda shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jigo cikin zaman aka dama da shi daga can garin Daura inda ke zaman hutun mako guda.

Ministan ta bayyana cewar iyakokin da aka bude a daidai wannan lokacin sun hada da iyakar Seme da ke shiyyar kudu maso yamma, iyakar Ilela da ke arewa maso yamma, iyakar Mfun da ke kudu maso kudu da kuma iyakar Maigatari da ke shiyyar kudu maso yamma.

Ministan ta ce, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawarar da kwamitin da aka kafa don duba iyuwar sake bude iyakoki ya bayar, wanda ya samu shugabancin Ministan kasuwanci da masana’antu, ministan cikin gida, kula da harkokin kasashen waje, babban mai bada shawara kan harkokin tsaro, kwantilola janar na kwastam da kuma shugaban hukumar kula da shige da fice.

“Kwamitin an daura masa alhakin bibiya da bada shawara ga shugaban kasa kan yiyuwar sake bude iyakokin kasar nan.

“Shugaban ya kuma amince da bude iyakoki guda hudu da suka hada da Seme, Ilela, Maigatari da iyakar Mfum.

“Dukkanin wadannan iyakokin guda hudu an bada umarnin bude su ne nan take, an bada umarnin bude su kafin nan da ranar 31 ga watan Disamba,” ta shaida.

Idan za ku iya tunawa dai a watan Agustan 2019 ne shugaban kasar ya bada umarnin kulle dukkanin iyakokin Nijeriya bisa yawaitar masu fasa gwabrin shigo da kayan abinci da makamai cikin kasar nan.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Mauludin ‘Yan Shi’a Ya Gudana A Legas

Next Post

Zulum Ya Gana Da Shugaban Chadi Kan ’Yan Hijirar Borno

RelatedPosts

Sheik Karibullah

Sheik Karibullah Ya Nada Alhaji Kabiru Sani Kwangila Khadimul Nabiyya A Taron Maulidin Gidansa

by Khalid Idris Doya
20 mins ago
0

A ranar Lahadi ne aka gudanar da Maulidin Manzon Allah...

Magance Matsalar Tsaro

In Dai PDP Na Son Samun Nasara, To Ta Sa Mata A Gaba – Amina Soba

by Khalid Idris Doya
25 mins ago
0

Hajiya Amina Adamu Soba, Tsohuwar 'yar takara ce a jam'iyyar...

Allurar Rigakafin Kurona

An Yi Kira Ga ‘Yan Nijeriya Da Su Rungumi Allurar Rigakafin Kurona Da Zarar An Fara

by Khalid Idris Doya
31 mins ago
0

An yi kira ga al"umar kasar nan su yi amfani...

Next Post
Yan Hijirar Borno

Zulum Ya Gana Da Shugaban Chadi Kan ’Yan Hijirar Borno

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version