Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Harin Boko Haram Ya Yi Kamari

Published

on

A ranar Talata ne a can birnin New York, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shelanta wa taron shugabannin duniya matsayin Nijeriya a kan wasu abubuwa da suka shafi sauran kasashen duniya.

Da yake bayyana matsayin na Nijeriya a ranar farko da aka bude tattaunawa a taro na 73 na Majalisar Dinkin Duniya, (UNGA73), tun da farko, Shugaban Kasan ya fara ne da yin jinjina da ta’aziyyar marigayi tsohon babban Sakataren Majalisar na Bakwai, Kofi Annan, kan irin gudummawar da ya bayar ta fuskacin samar da zaman lafiya a duniya.

A cewar Shugaba Buhari, “Mu a Afrika, a daidai lokacin da muke cikin jimamin rashin wannan gawutaccen dan namu, kuma shahararre a duniyar nan, muna kuma alfahari da irin hidimar da ya yi wa dan adam a wannan duniyar wanda har ya zama abin koyi nagari. Cikin natsuwa da kuma dagewa ne ya kai ga cimma manufofin sa na tabbatar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da hakkin dan adam. Shi ya kasance shugaba ne abin koyi, ya samar da fata tagari hatta a lokutan kalubale masu tsauri. Ya karar da rayuwar sa wajen yi wa al’umman duniya hidima. Muna farin ciki da zaman lafiyan da duniya ta samu a karkashin sa, madalla da irin wannan shugabancin na shi abin koyi.”

Shugaba Buhari ya yi nu ni da cewa, a shekarar da ta gabata, duniya ta ga wasu alamomi masu kyau da suke karfafa alamun fata tagari, wadanda aka cimmawa ta hanyar tattaunawar manyan shugabannin duniya wajen warware wasu rigingimu masu yin barazana ga zaman lafiya a duniya, ya yaba wa, “Kokarin da shugabannin kasashen Amurka, Koriya ta Arewa da Koriya ta kudu suka yi wajen ganin an cimma manufar raba shiyyar ta Koriya da makamin Nukiliya.”

Ya kuma yaba da kokarin samar da zaman lafiyan da Shugaba Donald Trump da Shugaba Kim Jong-Un, suke yi na gudanar da taro mai yawan tarihi a tsakanin su, ya kuma bukaci shugabannin biyu da su ci gaba da irin wannan taron abin yabawa a tsakanin su.”

Da yake bayyana damuwarsa a kan wasu abubuwan da suke yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, Shugaban kasan ya yi nuni da yadda wasu abubuwan suka kazance. “Ci gaba da da rikicin Rohingyas a Myanmar, rikicin Isra’ila da Palesdinawa da ya ki ci, ya ki cinyewa, yakin da ake yi a kasar Yemen, da Siriya, da kuma yakin da ake yi a sassan duniya, da ta’addancin ‘yan ta’adda kamar na Boko Haram da Al-Shabbab, duk abin damuwa ne.

A cewar Shugaba Buhari, “Ta’addancin ‘yan ta’adda da muke fuskanta musamman a yankunan Sahel da tafkin Cadi, yawanci a cikin gida ne ake ruruta wutar rikicin, wanda a yanzun kuma kungiyoyin ‘yan Jihadi na duniya ke kara ruruta shi, ta hanyar mayakan ‘yan ta’addan da suka gudo daga kasashen Siriya da Iraki da kuma makaman da aka wawasa daga rusasshiyar kasar Libiya.

“Akwai alamun kamar barnar ta yi sauki a yankin na Myanmar. Muna yaba wa kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wajen mayar da hankalin ta a kan halin da ake ciki a yankin na Myanmar, wajen kawo karshen wahalar da al’ummar yankin suke ciki, da kuma hukunta wadanda suka aikata mugayen laifukan a kan mutanan yankin da ba su ji ba, ba su gani ba, na al’ummar yankin da suka hada da mata da yara da kuma tsaffi.”

Ya kuma kirayi kasashen na duniya da su karfafa kokari wajen warware rigingimun kabilanci da na Addini a ko’ina ne a sassan duniyar nan, shugaba Buhari, ya nu na goyon bayansa ga kokarin da majalisar ta dinkin duniya ke yi na tabbatar da duk ‘yan gudun hijirar na Rohingya sun koma gidajen su a kasar ta Myanmar, tare da samar masu da tsaron da ya dace da kuma zaman su a matsayin ‘yan kasa a kasar su ta gado. Mun lura da alamun da gwamnatin kasar ta Myanmar ta nu na, na magance wadannan matsalolin, muna kuma karfafa su da su ci gaba a kan hakan.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: