Khalid Idris Doya" />

Buhari Ya Bukaci Kara Himma Don Yaki Da Tarin Fuka (TB)

Tarin Fuka

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su kara himma tare da hada karfi da karfe gami da bullo da sabbin dabarun kimiyya da na magani wajen yaki da cutar Tarin Fuka (TB) daya
daga cikin manyan cutukan da ke janyo mace-mace.

A sakonsa yayin tattaunawa kan hada karfi da karfe wajen yaki da cutar tarihin fuka ‘Global Stop TB Partnership’, shugaban Buhari ta cikin sanarwar manema labarai da Kakakinsa Femi Adesina ya fitar, ya nuna damuwarsa kan yadda yaki da cutar Korona ya jawo tangarda ga yaki da cutar ta tarin fuka a duniyance.

Ya ce, ya taba fada a wani babban taron ganawa da  majalisar dinkin duniya ta yi a shekarar 2018 kan bukatar da ke akwai na maida hankali kan tarin fuka, inda a cewarsa yanzu haka an fi tsananin bukatar maida hankali wajen shawo kan matsalar tarin fuka a duniya baki daya, ya nemi hukumomi, kungiyoyin kasa da kasa musamman a nahiyar Afrika da su kara maida hankali wajen shawo kan wannan matsalar.

“Nijeriya tana daga cikin kasa masu fama da cutar tarin fuka wanda aka rasa mutane da dama sakamakon kes din TB.”

Yana mai cewa gwamnatinsa ta maida sashin lafiya daga cikin fannoni masu muhimmancin kulawa inda ya ce sun samu nasarar rage kaifin cutar ta tarin fuka tun lokacin da suka amshi ragamar mulkin kasar nan.
Sannan, ya kuma ce an samar da asibitocin kula da masu cutar tarin fuka, cutar nan mai karya garkuwar jiki, maleriya da sauran cutukan yau da kullum da ke addabar jama’a domin maida hankali ga kula da
lafiyar ‘yan kasa.

Ya ce, suna kuma kokarin sake kudaden da suka dace wa sashin lafiya domin muhimman hakan garesu. Ya bada tabbacin gwamnatinsa na kara himma wajen cigaba da shawo kan cutar tarin fuka a tsakanin jama’a, sai ya nemi sauran kasashe da su cigaba da fito da dabarun kawar da wanan cuta domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Exit mobile version