Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Bukaci Lauyoyi Su Farfado Da Mutumcin Bangaren Shari’a

Published

on

Shugaba Buhari ya kalubalanci kungiyar Lauyoyi ta kasa da ta inganta tare da tsarkake sashen shari’a da cibiyoyin zabuka na kasar nan domin kyautatuwan mulkin Dimokuradiyyan kasar nan.
Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake shelanta bude taron shekara-shekara na wannan shekarar ta 2018, na kungiyar Lauyoyi ta kasa a Abuja ranar Lahadi.
Ya kuma bukace su da su yi aikin su domin samar da hadin kan kasa ta hanyar jawaban da za su gabatar a wajen taron, cikin al’umma, musamman ma dai a kotuna.
A cewar shi, yin wannan kiran ya zama tilas a daidai wannan lokacin da kasar nan ke sake shiga wani rukukin na siyasan babban zaben 2019.
Shugaba Buhari ya yi masu nu ni da cewa, za a iya yin aiki da hukumce-hukumcen shari’a ne kadai in kasa tana zaune lafiya.
Shugaban kasan ya tabbatar ma da Lauyoyin shawarar da gwamnatin sa ta yanke na habaka duk wani abu da ya shafi tattalin arziki wanda yin hakan ne zai samar da yanayin da ya dace na yin aikin na su.
Shugaban ya ce, “Mun ratso mawuyatan lokuta na farfado da tattalin arziki a farkon wannan gwamnatin a shekarar 2015.
“Yanzun mun zo lokacin da tattalin arzikin ke ta habaka, wanda ya hada da yadda asusun ajiyarmu na wajen ke ta kara cika, mun kuma yi watanni 13 a jere ba tare da an sami tashin farashin kayayyaki ba, fadada shirye-shiryen mu na kyautata rayuwar al’umma tare da toshe hanyoyin da suka jima suna tsotse mana tattalin arzikinmu duk a cikin shirinmu na farfado da tattalin arzikin.
Daganan sai Shugaba Buhari ya yi fatan Lauyoyin za su bayar da gudummawa wajen kyautatawa tare da bunkasa yanayin harkokin kasar nan ta hanyar girmama doka.
Ya kuma bukaci Lauyoyin da su bayar da na su gudummawar wajen farfado da sashen shari’a na kasar nan da fifita kasar nan a kan dukkanin son rayukan su wajen gudanar da ayyukan na su.
“Kotun mu ta koli ya kamata ta dauki wannan matsayin ta hanyar samar masa da matsaya ta
shari’a a duk inda wani abu ke yi ma tsaron kasar nan ko zaman lafiyarta barazana ko yake neman yi mata barazana, to ya zama tilas wannan abin ya kasance a mataki na biyu kasa da wannan hamshakiyar kasar ta mu da al’ummanta.
Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin samun nasarar taron Lauyoyin, sai ya bukaci Lauyoyin da su tattauna kan dukkanin al’amurra ta yadda za su karfafa dangantaka a tsakanin su.
Sai shugaban kasan ya yi amfani da wannan daman wajen bayyana irin matakan da gwamnatin sa ta dauka na tabbatar da alkinta albarkatun kasar nan.
“Ganin girman kalubalen da muka gada da kuma shaukin da al’umman mu ke da shi na samar da sabuwar hanyar tafiyar da al’amurran kasar nan, kalubalen mu na farko shi ne canza al’adar nan ta na fi karfin a bincike ni cikin hanzari a wajen tafiyar da albarkatun kasar nan, inda muka maye gurbin ta da al’adar bin diddigi da kuma aikata komai a bayyane.
“Muna bukatar tafiyar da albarkatunmu ta yadda za su amfani kowa, a maimakin son zuciya na wasu ‘yan kalilan.
“Don cimma wannan manufar, sai da muka yi watsi da tsohuwar al’adan nan wajen tafiyar da harkokin kasa, kamar yadda duk ku ka shaida a shekaru uku da suka gabata.
Ya kuma ce, tabbas gwamnati ta sami nasarori masu yawa a fannoni da dama, da suka hada da, wayar da kan jama’a bukatar kalubalantan duk wata nau’in cuwa-cuwa da sata a kasar nan.
“Sai dai a kan sami wasu tsiraru a cikin al’umma ciki har da wasu Lauyoyin da suka kasa yardan ma kansu da ire-iren canjin da muka kawo, duk kuwa da cewa suna da tabbacin wannan canjin mun kawo shi ne domin amfanin al’umma bakidaya.
“Babban abin bakin cikin shi ne, muna yakar sata a kasar nan, ita ma satar tana mayar mana da martani,” in ji shi.
Shugaban kasan ya taya sabbin shugabannin kungiyar Lauyoyin a karkashin jagorancin, Mista Paul Usoro murna, ya kuma yi masu fatan samun nasara a zamanin mulkin na su na ciyar da aikin Lauyoyin gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: