Buhari Ya Dawo Gida Bayan Taron Majalisar Dinkin Duniya A Amurka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso birnin tarayya Abuja da safiyar ranar Asabar jim kadan da bayan ya kammala halartar taron majalisar dinkin duniya na 74 da ya gudana a birnin New York dake kasar Amurka.

Da farko an tsara shugaban zai dawo da safiyar ranar Lahadi ne da misalin karfe 7, amma shugaban ya dawo da safiyar asabar.

Jirgin da ya dauko shugaban kasar yana dauke da sauran jami’an da suka raka shugaban kasar, inda ya sauka lafiya a sashen saukar shugaban kasa dake filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja.

Bayanai sun tabbatar da cewa abin da yasa shugaban kasar ya dawo a yau Asabar sabanin Lahadi saboda ya kammala duk wani abu da ya kai shi.

Buhari ya bar Nijeriya ne a ranar 22 ga watan Satumba.

 

Exit mobile version